'Ni Jan Biro ne Maganin Dakikin Yaro,' Gwamna Fubara Ya Jijjige Wike da Mutanensa
- Gwamnan jihar Ribas, Similanayi Fubara ya bayyana cewa a shirye yake ya cigaba da maganin masu kokarin kawar masa da hankali
- Fubara ya yi wannan jawabin ne a wani bikin addu'ar sabuwar shekara da aka gudanar a Cocin St. Paul’s Anglican a garin Opobo/Nkoro
- Malaman cocin sun jaddada bukatar amincewa da dogaro ga Allah, wanda shi kaɗai ke iya kawo nasara da ci gaba a jihar Ribas
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Similanayi Fubara, ya caccaki bangaren tsohon gwamnan jihar kuma Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike.
Gwamna Fubara ya bayyana haka ne yayin addu’ar sabuwar shekara da aka gudanar a wani coci a daren ranar 1 ga Janairu, 2025.
Daily Trust ta wallafa cewa mai magana da yawun gwamnan, Nelson Chukwudi ya tabbatar da cewa Fubara ya dogara ga Allah wajen fatattakar makiya jihar da al’ummarta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Fubara ya tabo Wike da mutanensa
A yayin bikin sabuwar shekara, Gwamna Fubara ya bayyana cewa makiyan jihar za su ci gaba da fuskantar gazawa a dukkan shirye-shiryensu.
Rahoton Vanguard ya nuna cewa Fubara ya ce har yanzu yana nan a matsayinsa na jan biro maganin dakikin yaro.
Fubara ya kara da cewa wakar da aka rera a lokacin taron ta kasance mai karfafa wa al’umma gwiwa domin su ci gaba da dogaro da Allah.
Malamai sun yi addu'a ga jihar Ribas
Babban Fasto a Kudancin Najeriya, Rabaran Emmanuel Oko-Jaja, wanda ya jagoranci addu’ar, ya ambaci kalubale da dama da suka faru a shekarar da ta gabata.
Faston ya ce duk da wadannan matsalolin, akwai bukatar mutane su dogara ga Allah domin samun nasara a sabuwar shekara.
Rabaran Oko-Jaja ya yi addu’ar zaman lafiya, haɗin kai, ci gaba da kuma ayyukan cigaban jihar da suka yi daidai da manufofin kasafin Ribas na 2025.
Gwamnan Bauchi ya yi martani ga Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Bauchi ya yi martani ga gwamnatin tarayya kan zarginsa da yin barazana da shugaba Bola Tinubu.
Sanata Bala Muhammad ya bayyana cewa abubuwan da ya fada gargadi ne a kan abin da zai iya faruwa a Najeriya kan kudirin haraji ba barazana ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng