"Muna Sa Rai Kwankwaso zai Dawo Cikinmu," PDP na Son Kwace Mulki daga Hannun Tinubu
- Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso na dab da samun tayin komawa jam'iyyar PDP domin tunkarar zaben 2027
- Mukaddashin shugaban PDP na kasa, Ambasada Umar Iliya Damagum ya bayyana cewa za su tuntubi Kwankwaso
- Ambasada Damagum ya kara da cewa dole su nemi hadin kan domin yin waje da gwamnatin Bola Tinubu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Babbar jam’iyyar hamayya ta PDP ta ce akwai shirye-shirye da ta yi na ganin ta yi nasarar kwace mulki daga hannun APC a zaben 2027.
Mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa Umar Iliya Damagum ne ya bayyana cewa daga cikin yadda suke son cimma burinsu akwai gayyatar tsofaffin ‘yan jam’iyya.
A hira da ya yi da BBC Hausa, Mukaddashin shugaban jam’iyyar na ganin guda daga cikin wadanda za su yi zawarcinsu shi ne Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jam'iyyar PDP za ta nemi Rabiu Kwankwaso
Jaridar Aminiya ta ruwaito Damagum na cewa zai yi wuya babbar jam’iyyar adawa ta sake nasara a zabe mai zuwa saboda wasu dalilai.
Ya kara da cewa;
“Nan ba da jimawa ba za mu tuntuɓi Kwankwaso, kuma har gobe ba ma cire tsammanin zai iya zuwa PDP, a yi tafiya da shi mu karkaɗe jam’iyyarmu mu fuskanci wannan azzalumar gwamnati.”
Damagum ya fadi yadda Kwankwaso ya bar PDP
Ambasada Umar Iliya Damagun ya tabbatar da kalaman Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso na cewa an yi masu wulakanci gami da cin fuska a PDP.
Ya ce wannan shi ne dalilin da ya sa Kwankwaso da tawagarsa su ka fice daga PDP a wancan lokaci, duk da cewa shi ma ya yi bakin kokarin lallashinsa, amma abin ya ci tura.
Kwankwaso ya yi watsi da batun 'maja'
A baya, mun ruwaito cewa Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya musanta rahotannin da ke cewa ya kulla wata yarjejeniya da tsofaffin 'yan takarar shugaban kasar nan.
Sanata Kwankwaso ya ce babu kamshin gaskiya a cewar sun amince da karba-karba ko raba wa'adin mulkin kasar nan a tsakaninsu domin hade wa wajen tunkarar APC a 2027.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng