Yadda Muka Shirya Fitar da Tinubu daga Aso Rock a 2027, Jigon PDP Ya Yi Bayani

Yadda Muka Shirya Fitar da Tinubu daga Aso Rock a 2027, Jigon PDP Ya Yi Bayani

  • Kakakin matasan PDP na kasa, Dare Glintstone Akinniyi, ya ce PDP za ta nuna wa APC hanyar ficewa daga Aso Villa a 2027
  • Akinniyi ya ce APC jam’iyya ce da ta gaza, ta na rike da mulki ba tare da shiri ko wata dabarar kawo cigaba a Najeriya ba
  • A wata hira ta musamman da Legit.ng, kakakin matasan ya ce PDP ce kadai jam’iyyar da za ta iya kawar da APC daga mulki a 2027

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kakakin kungiyar matasan jam'iyyar PDP na kasa, Dare Glintstone Akinniyi, ya ce PDP za ta yi babban shiri a 2025 domin kalubalantar APC.

Dare Akinniyi ya bayyana cewa ’yan Najeriya su sa ran ganin gyara da tsabtace PDP a shekarar 2025 da za a shiga.

Kara karanta wannan

"Dalilinmu na daga wa gwamnati kafa," ASUU na shirin tsunduma yajin aiki

Jigo a jam'iyyar PDP ya yi magana kan shirin da suke yi na hambarar da Tinubu a zaben 2027
Jigon PDP, Dare Akinniyi ya fadi shirin jam'iyyar na fitar da Tinubu, APC daga Aso Villa a 2027. Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Jam'iyyar PDP za ta yi babban shiri kan APC

Ya yi wannan jawabi ne a wata hira ta musamman da jaridar Legit.ng ta yi da shi a ranar Lahadi, 29 ga watan Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, PDP ita ce jam’iyya daya tak da za ta iya kawar da APC daga kan mulki a kasar nan.

Kakakin kungiyar matasan ya ce a 2025, ’yan Najeriya su shirya ganin yadda PDP za ta yi adawa mai karfi, tare da hana APC sakat.

"PDP za ta fitar da APC daga Aso Villa" - Akinniyi

Akinniyi ya ce bukatar da ake da ita ita ce PDP ta zamo mai karfi da hadin kai, domin ba ta zarrar nuna wa APC hanyar ficewa daga Aso Villa a zaben 2027.

"Duk da cewa jam'iyyar tana cikin yanayi na rikici a yanzu, amma za ta fita kuma za ta dawo da tasirinta a shekarar 2025."

Kara karanta wannan

Gawurtattun ‘yan siyasa 6 da suka bar adawa, suka koma jam’iyyar APC a shekarar 2024

- A cewar kakakin matasan.

Ya sake nanata cewa PDP ita ce jam'iyya daya tilo da za ta iya ganin bayan APC a zaben 2027, amma sai ta gyara rigingimun cikin gidanta.

PDP za ta raba hanya da 'yan siyasarta

Kakakin matasan ya ce:

"Muna ganin cewa APC jam'iyya ce da ta gaza, wadda ke gudanar da mulki ba tare da wani shiri ko dabarar cigaban Najeriya ba."

Ya kara da cewa PDP za ta zama madadin wannan jam’iyya da ta nuna gazawarta a mulki, tare da zama jam’iyyar da za ta cika muradun jama’a.

"A 2025, PDP za ta aiwatar da tsabtace jam’iyya, inda za a raba hanya da ’yan siyasa masu amfani da PDP don biyan bukatun kansu."

- A cewar Dare Akinniyi.

2027: Babba a PDP ya ba jam'iyyar mafita

A wani labarin, mun ruwaito cewa Adetokunbo Pearse, tsohon dan kwamitin yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar a 2023 ya ba PDP shawara kan zaben 2027.

Kara karanta wannan

'Dalilin da ya sa Atiku da 'yan Arewa ba za su kayar da Tinubu a 2027 ba,' Okupe

Kusa a PDP, ya ce jam'iyyar za ta iya samun nasara kan APC da sauran jam'iyyun siyasar kasar nan a 2027 idan aka ba dan Kudu tikitin takarar shugaban kasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.