Tsohon Hadimin Jonathan Ya Soki El Rufa'i kan Zargin Kabilanci a Gwamnatin Tinubu

Tsohon Hadimin Jonathan Ya Soki El Rufa'i kan Zargin Kabilanci a Gwamnatin Tinubu

  • Tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri ya yi tir da ikirarin cewa Mai girma Bola Ahmed Tinubu yana da kabilanci
  • An yi zargin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya fi nada ‘yan kabilarsa, wato Yarbawa a manyan mukamai a hukumomi masu gwabi
  • A raddin da ya yi, Omokri ya fusata da masu sukar da suka zargi shugaba Tinubu da fifita kabilar Yarbawa wajen nade-nade a gwanatinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT AbujaTsohon hadimin shugaban ƙasa, Reno Omokri, ya bayyana ikirarin cewa mutanen Yarbawa ne ke shugabantar muhimman hukumomin Najeriya a matsayin “marasa tushe.”

A cewarsa, waɗannan zarge-zargen na iya haddasa rikicin kasuwar sauyin kudi na kasuwar hannun jarin Najeriya (NSE) ta hanyar haddasa rashin daidaito.

Kara karanta wannan

Adon da Aisha Buhari ta caba a bikin al'adun Kalaba ya ja hankali

Omokri
Hadimin Jonathan ya caccaki El Rufa'i Hoto: Reno Omokri/Nasir El Rufai
Asali: Facebook

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Omokri ya kara da cewa shugaba Bola Tinubu yana yin adalci wajen nade-nade, domin dan Arewa maso Gabas ne ke jagorantar NNPCL.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

El-Rufai na zargin gwamnatin Tinubu da kabilanci

Legit ta ruwaito cewa tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya tofa albarkacin bakinsa kan sukar da Farfesa Farooq Kperogi ya yi game da fifikon kabilanci wajen nade-nade a gwamnatin Tinubu.

Da fari, Kperogi ya zargi Tinubu da naɗa Yarbawa a manyan mukamai a hukumar man fetur, lamarin da Nasir El-Rufa’i ke ganin bai dace ba a rika nuna kabilanci.

“Shugaba Sinubu ba shi da kabilanci,’ – Omokri

Reno Omokri, wanda aka sani da goyon bayan gwamnatin Tinubu, ya ce ban da NNPCL, sauran hukumomi suna karkashin jagorancin wadanda ba Yarbawa ba.

Ya ce:

“A Najeriya, ban da NNPCL, hukumar tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya (NPA), hukumar filayen jiragen sama ta Najeriya (FAAN), hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC), hukumar kula da jiragen ruwa da tsaro ta Najeriya (NIMASA), da hukumar inshorar adana kudaden Najeriya (NDIC), su ne manyan masu kawo kudaden shiga ga gwamnatin tarayya. Daga cikin waɗannan hukumomi guda shida (idan aka haɗa NNPCL), biyu ne kawai ke karkashin mutanen Kudu maso Yamma."

Kara karanta wannan

Tchiani: An samu bayanai daga kasar waje kan zargin Najeriya da hada kai da Faransa

Gwamnan Tinubu ya ziyarci Tinubu

A baya, mun ruwaito cewa gwanan Filato, Caleb Muftwang ya kai ziyara ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da ke hutun karshen shekara a Legas, suka tattauna batutuwa.

Gwamna Muftwanga ya yaba da kokarin da shugaban kasar ke yi wajen tabbatar da tsaro a Najeriya, daga ciki har da jiharsa da ya ce ana samun kwanciyar hankali a yanzu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.