Kwankwaso Ya Fadi Gaskiya kan Cimma Yarjejeniya Tsakaninsa da Atiku, Peter Obi
- Dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NNPP a zaɓen 2023, ya yi martani kan cimma yarjejeniya tsakaninsa da Atiku Abubakar da Peter Obi
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa babu wata yarjejeniya da ya cimma tsakaninsa da su biyu kan wa'adin da za su yi a mulki
- Kwankwaso ya nuna cewa maganar ta ƙona masa rai domin bai kamata a ce dattawa suna faɗin abin da ba haka yake ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya fito ya yi magana kan batun cimma yarjejeniya tsakaninsa da Atiku Abubakar da Peter Obi kan wa'adin da kowannensu zai yi a mulki.
Madugun na Kwankwasiyya ya musanta cewa akwai yarjejeniya tsakaninsa da ƴan takarar shugaban ƙasa na zaɓen 2023, kan cewa dukkaninsu za su yi mulki na wani wa'adi.

Asali: Facebook
Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da sashen Hausa na RFI.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Kwankwaso ya ce kan yarjejeniya da Atiku, Obi?
Tsohon gwamnan na jihar Kano ya bayyana cewa ko kaɗan bai san an yi hakan ba, kuma babu ƙamshin gaskiya a ciki.
Sai dai, ya ce labari ya riske shi cewa ɓangaren Atiku Abubakar ne ke yaɗa wannan maganar inda suke yin zama tare da shugabanni da suka haɗa da malamai suna gaya musu hakan.
Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa maganar ta ƙona masa rai domin bai kamata a ce dattawa su riƙa fitowa suna yin ƙarya ba.
"Wannan magana ta ƙona mani rai matuƙa, a ce dattawa suna ƙarya, suna faɗar abin da ba a yi ba, an faɗa mani an tara kusan malamai 45 ana gaya musu wannan magana wacce babu ita, ko kaɗan ban ji daɗin wannan abu ba."
"An gaya musu wai na amince cewa Atiku zai yi shekara huɗu, ni ma zan yi hudu, wancan shi kuma Peter Obi ya yi shekara takwas, wannan maganar babu ita, ba a yi ta ba."
- Rabiu Musa Kwankwaso
Kwankwaso ya samu nutsuwa bayan barin PDP
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan na jam'iyyar NNPP ya bayyana cewa barin PDP da ya yi zuwa NNPP ya sanya ya samu nutsuwa.
Kwankwaso ya ƙara da cewa a yanzu ya huta da wulaƙancin da aka yi masa a PDP da shi da mutanensa.
Kwankwaso ya ba ƴan majalisa shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya shawarci ƴan majalisar NNPP kan ƙudirin haraji na gwamnatin Bola Tinubu.
Rabiu Musa Kwankwaso ya buƙaci ƴan majalisar tarayya na jam'iyyar NNPP da su yi adawa da ƙudirin domin ganin ya ƙi zama doka.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng