Sule Lamido Ya Fadi Abin da Tinubu Ke Boye Wa Yan Najeriya, Ya Gano Laifin Buhari

Sule Lamido Ya Fadi Abin da Tinubu Ke Boye Wa Yan Najeriya, Ya Gano Laifin Buhari

  • Tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido ya zargi gwamnatocin APC da rashin gaskiya ga 'yan Najeriya game da halin da kasar ke ciki
  • Tsohon gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin PDP ta fi bayyana gaskiya da halin da ake ciki a mulkinta
  • Lamido ya ce gwamnatin Tinubu tana cike da sakaci da son rai wajen amfani da basussuka ba tare da bayyana gaskiya ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Jigawa - Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya magantu kan salon mulkin Bola Tinubu.

Lamido ya zargi Shugaba Bola Tinubu da rashin bayyanawa 'yan Najeriya gaskiya game da halin da kasar ke ciki da mulkinsa.

Sule Lamido ya zargi gwamnatocin Tinubu da na Buhari
Sule Lamido ya koka kan rashin gaskiya a mulkin Bola Tinubu da Muhammadu Buhari. Hoto: Sule Lamido, Asiwaju Bola Tinubu, Muhammadu Buhari.
Asali: Facebook

Lamido ya soki gwamnatocin Tinubu, Buhari

Lamido ya bayyana wannan zargin ne a lokacin da ya ke hira da yan jaridu kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya ziyarci Tinubu a Legas, an ji abin da suka tattauna a cikin bidiyo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon gwamnan wanda yake babban jigo a jam'iyyar PDP, ya kuma tabo Muhammadu Buhari inda ya zarge shi da rashin bayyana gaskiya ga 'yan Najeriya.

Sule Lamido ya ce gwamnatocin Buhari da Tinubu sun fi mayar da hankali kan farfaganda maimakon bayyanawa 'yan Najeriya halin da ake ciki, sabanin lokacin mulkin PDP.

"Gwamnatocin Buhari da Tinubu ba su bayyana gaskiya ga 'yan Najeriya, sabanin lokacin da PDP ke mulki, inda komai ke a bayyane ga kowa."
"Amma tun da Buhari ya hau, ya mayar da yaudara da farfaganda kayan aiki wajen gudanar da gwamnati."

- Sule Lamido

Lamido ya koka da rashin gaskiyar APC

Lamido ya kuma soki basussukan da Tinubu ke neman dauka, yana cewa:

“Abin da gwamnati ke fada wa 'yan Najeriya ba shi ne abin da take aiwatarwa ba.”
"Idan an gaya wa 'yan Najeriya gaskiya, babu laifi a hakan, amma ya za a yi a tsara kasafin Naira tiriliyan 30, a samu Naira tiriliyan 50, sannan a nemi bashin da ya fi karfin ribar da aka samu?"

Kara karanta wannan

Rashin nadamar cire tallafin fetur da abubuwa 3 da Tinubu ya fada a kan manufofinsa

- Cewar Sule Lamido

Lamido ya sake caccakar Tinubu

Kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa ya yi wa shugaban ƙasa Bola Tinubu wankin babban bargo bayan ya shilla zuwa ƙasar Burtaniya.

Sule Lamido ya caccaki matakin da Bola Tinubu ya ɗauka na tafiya hutun kwanaki 14 alhali ana cigaba da fama da matsin rayuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.