'Abin da Ya Sa Tinubu Zai Sake Lashe Zaben 2027 da Za a Gudanar a Najeriya'
- Hadimin tsohon shugaban kasa, Reno Omokri ya yi magana kan zaben 2027 da damar Shugaba Bola Tinubu
- Reno Omokri ya bayyana cewa Tinubu zai sake lashe zabe a 2027 saboda iya juya da abokan gaba zuwa abokai
- Omokri ya yaba da hazakar Tinubu wajen yin sulhu da tsofaffin abokan gaba don cimma burinsa na siyasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon mai ba shugaban ƙasa shawara ya ce ya tabbata cewa Bola Tinubu zai iya ba da mamaki a zaben 2027.
Reno Omokri ya ce Tinubu ya yi kokarin tabbatar da haɗin kai wanda zai taimake shi domin tazarce a zabe mai zuwa.
Reno Omokri ya yabawa salon siyasar Tinubu
Omokri ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X a yau Asabar 28 ga watan Disambar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Reno Omokri ya bayyana Bola Tinubu a matsayin shugaba mai ƙwarewar fahimtar halayyar ɗan Adam.
Ya ce Tinubu na da basirar juya abokan gaba zuwa abokai, kuma wannan zai taimaka masa wajen sake samun nasara a 2027.
Omokri ya yaba da kwarewar Tinubu wajen yin aiki tare da waɗanda suka kasance abokan gabansa a baya.
2027: Manyan dalilai da zai ba Tinubu nasara
Tsohon hadimin ya bayyana wannan a matsayin muhimmin dalili da zai tabbatar da nasarar Tinubu.
Shugabannin da suka dace suna iya yin sulhu da abokan gaba, sai dai idan bambancin ra’ayi, kamar addini, ya gaza warwarewa."
"Abokan gaba da ka juyo zuwa abokai sun fi amana fiye da abokai."
"Wannan dalili ne yasa nake tabbatar wa Shugaban Najeriya, Asiwaju Ahmed Tinubu, zai sake lashe zabe a 2027."
- Reno Omokri
'Tinubu ya dara Buhari a mulki' - Reno Omokri
A baya, kun ji cewa tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri, ya ce "shekara daya da Bola Tinubu ya yi, ya fi shekaru takwas na Muhammadu Buhari".
Omokri ya yi kwatancen ne bayan wani bankin hannun zuba jari ya ayyana Naira a matsayin kudin da ya fi tabuka abin kirki a duniya a watan Afrilun 2024.
Asali: Legit.ng