"Ka Daina Shiga Harkokinmu": Jam'iyyar APC Ta Gargadi Wani Gwamnan Najeriya

"Ka Daina Shiga Harkokinmu": Jam'iyyar APC Ta Gargadi Wani Gwamnan Najeriya

  • Jam'iyyar APC ta gargadi gwamnan jihar Ribas Similanayi Fubara da ya yi hattara kan shiga harkokinta a jihar ko ta dauki mataki
  • Shugaban APC na Ribas, Cif Tony Okocha ya zargi Fubara da daukar nauyin wasu daga cikin shari'un da jam'iyyar ke fuskanta
  • Sai dai, Gwamna Similanayi Fubara bai dauki wannan zargin na APC da wasa ba, inda ya mayarwa jam'iyyar martani mai zafi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ribas - Shugaban jam'iyyar APC a Ribas, Cif Tony Okocha, ya zargi Gwamna Similanayi Fubara da tsoma baki cikin harkokin jam’iyyar a jihar.

Cif Okocha ya ce Fubara yana daukar nauyin wasu shari'ar da ake yi da APC a jihar, yana mai gargadin cewa ka da ya ci gaba da yin haka.

Shugaban jam'iyyar APC ya yi magana kan tsoma bakin gwamnan Ribas a harkokinta
Jam'iyyar APC ta zargi gwamnan Ribas da tsoma baki a harkokinta. Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

APC ta gargadi gwamna kan shiga harkokinta

Kara karanta wannan

"Akwai lauje cikin nadi," Atiku ya zargi gwamnati da siyasantar da alkaluman NBS

Shugaban jam'iyyar ya tambayi dalilin da ya sa Fubara ba zai yi amfani da karfinsa wajen gyara PDP ba, maimakon shiga harkokin APC a cewar rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Cif Okocha ya ce:

“Ina masa addu’ar ya sauya hali, idan ba haka ba, fushin Allah zai iya sauka a kansa.”

Ya kara da cewa:

“Ya kamata ya yi amfani da wannan karfin nasa wajen gyara PDP, ko da yake yanzu ba shi da jam’iyyar siyasa.”

Gwamna Fubara ya mayar wa APC martani

Okocha ya ce Fubara ba zai iya samun goyon bayan PDP ba saboda ba shi da rijista da jam’iyyar, duk da yana kokarin bata APC.

Sai dai Fubara ya yi martani ta bakin mai ba shi shawara kan kafafen yada labarai, Jerry Omatsogunwa, inda ya ce bai da lokacin tsoma baki cikin harkokin APC.

Omatsogunwa ya ce Fubara cikakken dan jam’iyyar PDP ne kuma yana halartar taron gwamnoninta tare da gargadin Okocha kan kalamansa.

Kara karanta wannan

Shugaban PDP na fuskantar matsala daga Arewa, za a raba shi da kujerarsa

APC ta zargi Fubara kan kaddamar da ayyuka

A wani labarin, mun ruwaito cewa jam'iyyar APC ta yi ikirarin cewa wasu ayyuka da gwamnan Ribas, Similanayi Fubara ya ke kaddamarwa ba shi ne ya yi su ba.

APC ta ce da yawa daga cikin ayyukan da Fubara ke kaddamarwa, tsohon gwamnan jihar, kuma ministan Abuja, Nyesom Wike ne ya yi kafin ya sauka daga mulki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.