'Ba Ka Isa ba': Ciyamomi 18 Sun Yi Turjiya da Gwamna Ya Dakatar da Su a Jiharsa

'Ba Ka Isa ba': Ciyamomi 18 Sun Yi Turjiya da Gwamna Ya Dakatar da Su a Jiharsa

  • Kwana daya bayan Majalisar Edo ta dakatar da shugabannin kananan hukumomi, sun kalubalanci gwamna
  • Shugabannin kananan hukumomi 18 da ke jihar sun yi Allah wadai da matakin inda suka ce an saba doka
  • Wannan na zuwa ne bayan Majalisar ta dakatar da su da mataimakansu a jiya Talata 17 ga watan Disambar 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugabannin Kananan hukumomi 18 na jihar Edo sun yi Allah wadai da dakatar da su aka yi.

Dakatattun shugabannin sun ce matakin ya saba da hukuncin Kotun Koli kan ‘yancin kananan hukumomi.

Ciyamomi sun bijirewa umarnin Gwamna na dakatar da su
Shugabannin kananan hukumomi a Edo sun kalubalanci gwamna Monday Okpebholo bayan dakatar da su. Hoto: Sen. Monday Okpebholo.
Asali: Twitter

Edo: Ciyamomi sun kalubalanci dakatar da su

Punch ta ce shugabannin kananan hukumomi sun nuna damuwa kan dakatar da su da Majalisar Dokokin jihar Edo ta yi.

Kara karanta wannan

Kwana 1 ga barazanar Turji, an yi kazamar fada tsakanin yan bindiga, an rasa rayuka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugabannin da mataimakansu, sun kuma ambaci hukuncin da Alkalin Alkalai na jihar Edo ya zartar da wani umarnin kotu na hana daukar wani mataki a kansu.

Shugaban kungiyar (ALGON) reshen Edo, Newman Ugiagbe ya ce wa’adin su, wanda ya fara a ranar 4 ga Satumba 2023, zai kare ne a Satumba 2026.

Ugiagbe wanda kuma shi ne shugaban karamar hukumar Orhionmwon ya ce an zabe su ne ta dimokuradiyya, ba nadin gwamnati ba.

“Siyasa daban ce da mulki, abin da ke faruwa yanzu siyasa ce, amma mu samfurin doka ne, mutanen gari ne suka zabe mu."

- Newman Ugiagbe

Korafin gwamna kan shugabannin ƙananan hukumomin

A cewar Ugiagbe, dakatarwar tasu ta samo asali ne daga wani korafi da Gwamna Monday Okpebholo ya gabatar.

Gwamnan ya zargi shugabannin da aikata munanan laifuka, yana mai nuna sashe na 10(1) na dokar kananan hukumomi ta jihar Edo (2000).

"Kotu ta ayyana sashe na 10(1) na dokar kananan hukumomi ta jihar Edo ta shekarar 2000 a matsayin mai sabawa doka, mara inganci kuma ba daidai ba."

Kara karanta wannan

Majalisa ta dakatar da shugabannin ƙananan hukumomi 18 da mataimakansu

"Duk wani umarni daga gwamna na rushewa ko dakatar da shugabannin da aka zaba kafin cikar wa’adinsu ya zama haramtacce,”

- Newman Ugiagbe

Shugabannin sun bukaci hukumomin tsaro na ‘yan sanda da DSS da NSCDC da su kare dukiyar kananan hukumomi tare da tabbatar da bin umarnin kotu.

Gwamna ya dakatar da shugabannin kananan hukumomi

Kun ji cewa Majalisar dokokin Edo ta dakatar da shugabannin kananan hukumomi 18 na jihar bisa zargin almubazzaranci da rashin ɗa'a.

Wannan mataki ya biyo bayan wasiƙar da Gwamna Okpebholo ya aika majalisar, yana mai cewa ciyamomin sun ƙi kawo masa rahoton kudi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.