Ana Neman Obasanjo, IBB, Buhari, Jonathan Su Hadu, Su Kifar da Tinubu a 2027
- Tsohon jigo a APC, Salihu Lukman ya bukaci tsofaffin shugabannin Najeriya su haɗa kai domin ƙirƙirar sabuwar jam’iyya
- Salihu Lukman ya ce wannan jam’iyya za ta taimaka wajen samar da shugabanni masu bin Allah a 2027 idan suka kifar da APC
- Dan siyasar ya bayyana cewar rashin samar da jam'iyyar da za ta kara da APC tamkar goyon bayan wa’adin Tinubu na biyu ne
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja, Nigeria - Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC na Arewa maso Yamma, Salihu Lukman ya rubutawa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo wata budaddiyar wasiƙa.
A wasikar, Salihu Lukman ya nemi Obasanjo ya haɗa kai da tsofaffin shugabannin kasa domin kafa sabuwar jam’iyya da za ta kalubalanci Bola Tinubu da APC a babban zaɓen 2027.
Vanguard ta wallafa cewa Lukman ya yi kiran ne biyo bayan wata hira da aka yi da Obasanjo, ya yi tsokaci kan lalacewar shugabancin Bola Tinubu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lukman ya nemi a yi taron dangi ga Tinubu
A cikin wasikar, Lukman ya nemi hadin kan Janar Yakubu Gowon, Muhammadu Buhari, Janar Ibrahim Babangida da Janar Abdulsalami Abubakar.
Ya kuma hada da Goodluck Jonathan a kan su yi amfani da tasirin su wajen haɗa kai da shugabannin ‘yan adawa domin samar da jam’iyya mai karfi da za ta kifar da APC.
A cewarsa, bai kamata kawai a yi korafi kan shugabannin da suka gaza ba, kamata ya yi a hada karfi a kayar da su.
Lukman ya ce APC ta lalace a yanzu
Lukman ya bayyana cewa rashin bin ƙa’idojin mulki da rashin adalci ne suka lalata APC duk da irin damar da ta samu a 2015.
Ya ce, idan ba a gyara tsarin siyasa a ƙasar nan ba, za a ci gaba da samun shugabanni marasa bin Allah, waɗanda ke jagorantar ƙasar cikin rashin gaskiya.
Ya ƙara da cewa lokaci ya yi da tsofaffin shugabanni za su yi amfani da ƙarfinsu wajen ceto ƙasar daga shugabanci na rashin adalci.
Jam'iyyar APC ta ce Tinubu zama 'daram' a 2027
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC ta yi martani mai zafi a kan wata ziyara da Sanata Rabi'u Kwankwaso ya kai ga Obasanjo.
Jam'iyyar APC ta ce duk wani taro ko hadaka da 'yan adawa za su yi ba za su hana shugaba Bola Ahmed Tinubu samun nasara a 2027 ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng