Abba Gida Gida Ya Aikowa Kwamishinonin Kano da Umarni bayan Zazzaga a Gwamnati
- Gwamnan jihar Kano ya umarci kwamishinonin da aka canza su shiga ofis nan da ranar Talata mai zuwa
- Sanusi Bature DawakinTofa ya sanar da cewa kowane kwamishina zai kama aiki kafin zaman majalisar SEC
- Abba Kabir Yusuf ya na so duka kwamishinonin da aka canzawa ma’aikatu su mika takardun sallama
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kano - Alhaji Abba Kabir Yusuf ya turo da sabon umarni zuwa ga kwamishinoni kwanaki biyu bayan ya yi sauye-sauye a mulki a jihar Kano.
Mai girma Gwamnan jihar Kano wanda da alama har yanzu yana kasar waje, ya sallami kwamishinoni da wasu jami’an gwamnati.
Gwamna Abba ya fitar da sanarwa ga kwamishinoni
Sanarwa ta fito daga Sanusi Bature Dawakin Tofa a shafin Facebook cewa an umarci kwamishinonin da aka sauya su kama aiki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan Kano bukaci kwamishinonin da aka canzawa ma’aikata su gabatar da takardun karbar ofis ga wadanda za su canje su.
Sannan Abba Kabir Yusuf ya fadawa kwamishinonin su fara aiki gadan-gadan a sababbin ma’aikatun da aka tura su a jihar Kano.
Sanarwar ta ce dole kowane kwamishina ya mika takardu kuma ya shiga ofis domin kama aiki kafin a tashi aikin ranar Talata mai zuwa.
Za a ga sauyi a majalisar zartarwar Kano
Daga yanzu zuwa 17 ga watan Disamba 2024 za a ga sauye-sauye a ma’aikatu kamar yadda aka gani a shafin Salisu Hotoro a Facebook.
Sanusi Dawakin Tofa ya shaida cewa canje-canjen da aka yi zai tabbata a lokacin da majalisar zartarwa za ta zauna ranar Laraba.
Gwamnan ta bakin mai magana da yawunsa ya ce za a yi zaman majalisar SEC da ta kunshi kwamishinoni a ranar 18 ga Disamba.
"Duka kwamishinonin da canjin ya shafa za su mika ragamar aikin da yake hannunsu daga Litinin, 16 ga wata zuwa Talata, 17 ga watan Disamban 2024."
- Sanusi Bature D/Tofa
Gwamnan ya kuma yi kira ga ‘yan majalisar kwamishinonin su ribanya kokarinsu domin nasarar gwamnatin da yake jagoranta a Kano.
Meyasa gwamna Abba ya tsige Bichi?
Dazu aka ji labari cewa Adnan Mukhtar Adam Tudunwada bai ganin rashin lafiya ta sa aka kori Dr. Abdullahi Baffa Bichi daga kujerarsa.
A cewarsa, ba haka nan Abba Kabir Yusuf ya kori manyan jami’ai da kwamishinonin jihar Kano ba, akwai sa hannun Rabiu Kwankwaso.
Asali: Legit.ng