'Arewa na Fushi da Kai': An Gargadi Tinubu Ya Gyara Tafiyarsa, Yankin na Neman Mafita
- Kungiyar matasa ta (AYCF) ta nuna damuwa kan mulkin Bola Tinubu musamman a Arewacin Najeriya
- Shugaban kungiyar, Alhaji Shettima Yerima shi ya tabbatar da haka inda ya ce akwai sauran lokaci da Tinubu zai iya gyarawa
- Hakan na zuwa ne yayin da ake ta korafi musamman kan sabon kudirin haraji daga Arewacin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Kungiyar tuntuba ta matasan Arewa (AYCF) ta yi magana kan zaben 2027 a Najeriya.
Kungiyar AYCF ta bayyana ra’ayinta game da batun kin amincewar da ake zargin Arewa na yi ga kudirin sake fasalin haraji.
Matasan Arewa sun koka kan mulkin Tinubu
Shugaban kungiyar, Alhaji Shettima Yerima shi ya bayyana haka a wata tattaunawa da ya yi da jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yerima ya ce akwai gazawar gwamnati wajen samun nasarar gabatar da kudirin, yana mai cewa akwai bukatar a gudanar da tattaunawa mai kyau tare da bayyana komai.
Har ila yau, Yerima ya tabo batun rashin jin dadi a yankin Arewa kan gwamnatin Tinubu.
Ya ce akwai bukatar a magance matsalolin tsaro da kuma wahalhalun tattalin arziki domin dawo da amincewar mutanen yankin.
2027: Matasan Arewa sun shawarci Tinubu
"Arewa na fushi da gwamnati, amma har yanzu gwamnati na da damar gyara lamura cikin kasa da shekaru biyu."
"Domin haka, wasu daga cikinmu ba za su yi gaggawar cewa Tinubu ba zai yi wa Arewa wani amfani ba."
"Mun san tafiyar tana da wahala, amma ya kamata mu ba shi damar gwada aikinsa sannan mu karfafa masa gwiwa."
- Yerima Shettima
Yerima ya ce dan bai yi wani abu da zai inganta rayuwar al’umma ba, wasu daga cikinsu za su iya hade kai da juyawa akalar kuri’unmu zuwa inda za mu samu mafita.
Ya ce yan Arewa za su zauna tare da masu ruwa da tsaki, su cimma matsaya sannan su nemi mafita.
Haraji: Dattawan Arewa sun ba Tinubu shawara
Kun ji cewa Kungiyar 'Arewa Consultative Forum' ta shawarci Gwamnatin Tarayya ta mayar da hankali a kan shawarwarin 'yan kasa kan batun haraji.
Jami'in hulda da jama'a na kungiyar reshen Kano, Alhaji Bello Sani Galadanchi ya bayyana cewa su na kara duba abin da kudirin ya kunsa.
Asali: Legit.ng