"Ya Cancanta," Tsohon Shugaban APC Ya Yi Magana kan Naɗa Ɗansa a Muƙami
- Sanata Adams Oshiomhole ya yi magana kan naɗin ɗansa a matsayin kwamishinan lafiya a jihar Edo
- Tsohon shugaban APC na ƙasa ya ce a baya ɗansa ya nemi tsayawa takara sau da dama amma ya hana shi saboda gudun surutu
- Sai dai a wannan karon Oshiomhole ya ce yana ganin ɗansa ya cancanci kujerar Gwamna Monday Okpebholo ya naɗa shi
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Edo - Sanatan Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole, ya ce dansa, Cyril, ya cancanci zama kwamishinan lafiya na jihar Edo da ke Kudu maso Kudu.
Oshiomhole, tsohon gwamnan Edo ya ce sau da dama ɗansa na neman tsayawa takara amma ya hana shi saboda gudun surutun da zai biyo baya.
Sanatan ya bayyana haka ne yayin da ya baƙunci shirin siyasa a yau na Channels tv ranar Laraba, 11 ga watan Disamba, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda ake surutu kan naɗa ɗan Oshiomhole
A watan Nuwamba, abokin Oshiomhole, Gwamna Monday Okphebolo ya nada Cyril a matsayin kwamishinan lafiya bayan ya karɓi rantsuwar kama aiki.
Nadin Likitan wanda ya samu horo a Amurka ya janyo ce-ce-ku-ce daga mutanen Edo, inda wasu ke cewa gwamna ya yi haka don sakawa Oshiomhole.
Da aka tambaye shi ko ya amince da nadin dansa a matsayin kwamishinan, tsohon gwamnan ya ce sai da ya nunawa Gwamna Okpebholo bai gamsu da naɗin ba.
Tsohon shugaban APC ya yi martani
A rahoton Punch, Oshiomhole, tsohon shugaban APC na ƙasa ya ce:
"Bai yi aiki a karkashina ba, watakila Gwamna Monday yana tare da shi, amma lokacin da nake gwamna ya nemi tsayawa takarar ɗan majalisar wakilai, na ce masa ban yarda ba."
"Ya ƙara dawowa a karo na biyu na ce masa ban yarda ba. Yanzu kuma gwamna ya ya ba shi muƙami, ni ina ganin ya cancanta. Duk da haka na nunawa gwamna damuwata."
"Amma na fahimci cewa a rayuwar nan, mutum yana da ikon juya ɗansa yadda yake so amma ban da lokacin da ya girma."
Oshiomhole ya koka kan albashin ma'aikata
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Edo kuma Sanata a APC, Adams Oshiomhole ya koka kan yadda ma'aikatan Najeriya ke kara talaucewa.
Adams Oshiomhole ya ce rashin biyan ma'aikata kudin da zai wadace su rayuwa yana iya zama barazana ga tsaron Najeriya.
Asali: Legit.ng