2027: Bayan Fara Kiran Jonathan Ya Gwabza da Tinubu, Jam'iyyar APC Ta yi Magana
- Jam’iyyar APC ta nisanta kanta daga wata ƙungiya mai suna Team New Nigeria (TNN), da ta buga hotunan shugaba Goodluck Jonathan a Kano
- An ruwaito cewa APC ta bayyana cewa ƙungiyar TNN ba ta da alaƙa da ita kuma 'yan kungiyar ba su da katin shiga APC kwata kwata
- Legit ta tattauna da wani dan jam'iyyar APC a jihar Gombe, Aminu Isa inda ya ce ba su jin tsoron takarar Jonathan a zabe mai zuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Jam’iyyar APC ta nisanta kanta daga ƙungiyar TNN, da ta yi fice a Kano bayan ta buga hotunan neman zaɓen tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan kan 2027.
Hakan ya biyo bayan iƙirarin kungiyar TNN na cewa ta balle daga APC ne dominn kafa sabuwar jam’iyya.
Punch ta wallafa cewa jagora a jam'iyyar APC ya ce ba su da alaka da kungiyar TNN balle ma a ce daga cikinsu ta balle.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanya hotunan takarar Goodluck Jonathan a Kano
A makon nan aka ga hotunan Jonathan a manyan wurare a Kano, ciki har da Gyadi-Gyadi, Kofar Nasarawa da State Road.
Vanguard ta wallafa cewa hotunan suna ɗauke da taken Team New Nigeria 2027; The Goodluck Nigeria Needs, wanda ya haifar da jita-jita kan yiwuwar dawowar Jonathan fagen siyasa.
APC ta yi martani kan zancen takarar Jonathan
Mataimakin Sakataren tsare-tsare na kasa na APC, Nze Chidi Duru ya ce ƙungiyar TNN ba ta da alaƙa da APC.
Haka zalika ya bayyana cewa Jonathan ba ya cikin tafiyarta, kuma a zaben da ya gabata ma an saya masa tikitin takara amma jam'iyya ba ta amince da hakan ba saboda ba dan APC ba ne.
Kungiyar TNN na shirin kafa jam'iyyar siyasa
Shugaban TNN, Modibbo Farakwai ya bayyana cewa ƙungiyar tana da niyyar jawo masu zaɓe miliyan 26 a faɗin ƙasa.
Modibbo Farakwai ya kara da cewa TNN na shirin yin rajista a matsayin jam’iyya a hukumar zaɓe ta kasa (INEC).
Legit ta tattauna da dan APC
Wani dan jam'iyyar APC a jihar Gombe, Aminu Isa ya zantawa Legit cewa a shirye suke su fiskanci takarar 2027.
Aminu Isa ya kara da cewa a cikin shirin da suke domin zaben, ba su jin tsoron wani dan takara kuma ba su tunanin akwai mai iya karawa da Tinubu ya kai labari a 2027.
Jam'iyyar APC ta kafa kwamitin sulhu
A wani rahoton, kun ji cewa jam’iyyar APC mai adawa ta kafa kwamitin sulhu mai mutum takwas domin daidaita rikice-rikicen cikin gida.
APC ta bayyana kwamitin ne yayin wani taro a Yola karkashin jagorancin mataimakin shugaban APC na Arewa maso Gabas, Mustapha Salihu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng