Rikicin Cikin Gida Ya yi Kamari a APC, An Kafa Kwamitin Sulhu
- Jam’iyyar APC mai adawa ta kafa kwamitin sulhu mai mutum takwas domin daidaita rikice-rikicen cikin gida a jihar Adamawa
- An bayyana kwamitin ne yayin taro a Yola karkashin jagorancin mataimakin shugaban APC na Arewa maso Gabas, Mustapha Salihu
- Rahotanni na nuni da cewa kwamitin zai fara aiki nan ba da jimawa ba domin karfafa hadin kai a jam’iyyar kafin zabukan gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Adamawa - Jam’iyyar APC ta kaddamar da kwamitin sulhu mai mutum takwas domin gyara tsarin jam’iyyar da warware rikice-rikice a jihar Adamawa.
An bayyana wannan mataki ne a ranar Laraba a Yola, yayin wani taro da mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin Arewa maso Gabas, Mustapha Salihu ya jagoranta.
The Nation ta wallafa cewa sakataren yada labarai na APC a Adamawa, Mohammed Abdullahi ya ce kwamitin na karkashin jagorancin Sanata Muhammed Mana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan kwamitin sulhun jam'iyyar APC a Adamawa
Sanarwar da Legit ta samu ta bayyana cewa kwamitin ya kunshi wasu jiga-jigai kamar Sanatoci Bello Tukur, Abubakar Girei, Binta Garba da Injiniya Martins Babale.
Sauran 'yan kwamitin sun hada da Hon. Yusuf Buba Yakubu, Dr. Bridget Zidon, da kuma Barista Isa Baba, wanda ke matsayin Sakataren kwamitin.
Aikin da ke gaban kwamitin sulhun APC
Aikin da aka dora wa kwamitin ya hada da warware matsalolin cikin gida, karfafa hadin kai tsakanin ’ya’yan jam’iyyar.
A yanzu haka dai kwamitin ya fara zama a Abuja kuma zai fara aikin sulhu kai tsaye a Adamawa nan ba da dadewa ba.
APC ta bukaci hadin kai a Adamawa
Taron da APC ta gudanar a Yola ya samu halartar shugabannin zartarwar jam’iyya na jiha, shugabannin jam’iyya na kananan hukumomi da kuma ’yan majalisar dokokin jiha.
A yayin taron, APC ta jaddada cewa hadin kai da fahimtar juna su ne mabuɗan nasarar jam’iyyar a zabukan gaba.
Jam’iyyar APC ta bayyana taron a matsayin ci gaba daga wani taron farko da aka yi a Abuja tare da mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Malam Nuhu Ribadu.
An rusa shugabannin da Ganduje ya nada
A wani rahoton, kun ji cewa rikicin APC ya kara ƙamari a jihar Benue yayin da wata kotu ta kori shugabannin riko da Abdullahi Ganduje ya naɗa.
An ruwaito cewa A ranar 21 ga watan Agusta, Ganduje ya naɗa shugabannin saboda rikicin shugabanci da jam'iyyar ke fama da shi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng