Shugaban APC Ya Cika Baki, Ya Fadi Jihar Kwacewa a Zaben 2027
- Jam'iyyar APC reshen jihar Rivers ta zaɓi sabon shugaɓa wanda zai ja ragamarta nan da shekara huɗu masu zuwa
- Tony Okocha ya zama sabon shugaban jam'iyyar APC mai adawa a jihar Rivers bayan an gudanar da zaɓe
- Sabon shugaban na APC ya bayyana cewa jam'iyyar za ta koma kan madafun ikon jihar a zaɓen 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Rivers - Jam’iyyar APC reshen jihar Rivers ta zaɓi Cif Tony Okocha a matsayin shugabanta.
APC ta zaɓi Cif Okocha ne tare da sauran waɗanda za su jagoranci al’amuran jam’iyyar nan da shekaru huɗu masu zuwa.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa zaɓen ya kasance ƙarƙashin jagorancin Dr. Adoye Omale wanda ya wakilci shugabannin APC na ƙasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban APC ya cika baki kan zaɓen 2027
A jawabinsa, Tony Okocha ya ce zaɓen nasa ya tabbatar cewa masu sukar APC, kan ba ta da haɗin kai kuma ba za ta iya gudanar da zaɓe cikin lumana ba, sun yi kuskure.
"Waɗanda suka ce APC ba za ta iya gudanar da zaɓe ba sun yi ƙarya. APC za ta gudanar tare da lashe zaɓe sannan ta jagoranci gwamnati a jihar Rivers."
"Abin da muke buƙata daga gare ku, shi ne ku ba mu goyon baya mu tabbatar da cewa mun kawar da gwamnati mara bin doka a jihar Rivers."
“A shekarar 2027, idan Allah Ya kai mu, za a yi zaɓe a jihar Rivers, kuma fatanmu a gare ku shi ne ku taimaka mana domin APC ta karɓi mulkin jihar Rivers.”
- Tony Okocha
Ndume ya yi barazanar barin APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa sanatan Borno ta Kudu, Muhammad Ali Ndume, ya ce a shirye yake ya bar APC mai mulki idan har shugabancin jam’iyyar suka ba shi damar hakan.
Sanata Ndume ya ce tun kafin yanzu ya yi niyyar ficewa daga APC amma ya haƙura saboda kyakkyawar alaƙarsa da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Legit.ng