Ana Ta Hasashen Hadakar Jam'iyyun Adawa a 2027, Atiku Ya Gana da Obi
- Ana ta zarge-zargen cewa jam'iyyun adawa na shirin yin haɗaka mai ƙarfi a 2027 domin kifar da Bola Tinubu a kan mulki
- A yau Asabar, dan takarar shugaban kasa a LP, Peter Obi ya ziyarci Atiku Abubakar a gidansa da ke jihar Adamawa
- Duk da ba a samu wasu ƙarin bayanai kan ainihin dalilin ziyarar ba, wasu na hasashen bai rasa nasaba da zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya karbi bakuncin Peter Obi a gidansa da ke jihar Adamawa.
Atiku wanda ya yi takara a zaɓen 2023 da aka yi ya karbi bakuncin Obi da ya takarar shugaban kasa a LP a yau Asabar.
Ana hasashen haɗaka mai ƙarfi a 2027
Wannan na kunshe ne a cikin wani faifan bidiyo da Atiku Abubakar ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Asabar 30 ga watan Nuwambar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne yayin da wasu ke ta hasashen jam'iyyun adawa na shirin yin haɗaka a 2027.
Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa jam'iyyun adawa suna kokawa kan yadda Bola Tinubu ke gudanar da mulkinsa.
Atiku ya gana da Peter Obi a Adamawa
Sai dai ba a gama samun matsaya ba kan hadakar da ake zargin jam'iyyun na yi musamman zaben wadanda za su tsaya takara.
Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto ba a samu ainihin dalilin zuwa Obi gidan Atiku Abubakar ba.
"Lokacin karin kumallo da abokina, Peter Obi a jihar Adamawa."
- Atiku Abubakar
Ana zargin Atiku, Kwankwaso na shirin haɗaka
Kun ji cewa shugabannin jam’iyyar PDP sun yi karin haske a kan tattaunawar da ake yi tsakanin Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso.
PDP ta bayyana cewa ana ci gaba da tattaunawa kan yiwuwar manyan 'yan siyasar uku su hade kansu domin tunkarar babban zaben 2027.
Mataimakin kakakin PDP na kasa, Ibrahim Abdullahi, ya fadi hakan a ranar Litinin, ya kuma yi magana kan shirin korar Tinubu da APC.
Asali: Legit.ng