NNPP da APC: Yadda Yan Siyasa ke Wasa da Masarautar Kano
A ranar 16 Nuwamba, 2024 ne aka gudanar da gagarumin biki a Kano, wanda ya hada malamai da yan siyasa manya da kananan daga sassan kasar nan da dama.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - An gudanar da da bikin diyar jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu'u Musa Kwankwaso da yaron Dahiru Mangal a fadar Sarki Muhammadu Sanusi II.
An yi haka ne duk da cewa ana takaddama a kan waye Sarkin Kano, lamarin da gwamnatin tarayya ta shiga tare da bayyana goyon bayanta muraran ga Sarki na 15, Aminu Ado Bayero.
Legit ta yi waiwaye yan siyasar da su ka halarci bikin, da yadda nan gaba kadan Mataimakin shugaban majalisa, Barau I Jibrin ke shirin sake tsokano maganar sahihancin Sarkin Kano a wannan rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kano: Yan siyasa sun halarci bikin diyar Kwankwaso
Jiga jigan yan siyasa ne su ka halarci bikin Dr. Aisha Rabi'u Kwankwaso da Injiniya Fahad Dahiru Mangal, wanda ya sake fito da darajar tafiyar Kwankwasiyya.
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo da bayyanar Kashim Shettima, wanda ya zama waliyyin ango ya dauki hankali matuka gaya.
Abin da ya fi jawo hayaniya shi ne yadda mataimakin shugaban kasa ya lashe amansa bayan ya kira Sarki Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano.
Wannan ta sa masu amfani da kafafen sada zumunta su ka rika murna da bayyana cewa 'gaskiya ta fito' kan batun masarautar Kano.
Kashim ya gyara kalamansa kan Sarkin Kano
Murna ka koma ciki ga wasu daga cikin magoya bayan Sarki Muhammadu Sanusi II bayan mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya canza kalamansa.
A gyararren sakon da ke a shafinsa na Facebook, ya ce sun halarci daurin auren a 'fadar sarkin Kano' a maimakon sakon da ya wallafa da fari na cewa a 'fadar sarkin Kano 16.'
Za a yi gagarumin biki a fadar Sarkin Kano
A watan Disamba 2024 ne mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin zai aurar da yaransa biyu, kuma za a gudanar da bikin daya daga ciki a fadar sarkin Kano.
Wannan ya kara nuna barakar da ke tsakanin masarautar Kano, ganin yadda yan siyasar APC da PDP ke kiran wanda su ke kauna a matsayin 'Sarki.'
Yadda masana ke kallon rikicin masarautar Kano
Dr. Ibrahim Ado Kurawa, guda ne daga cikin 'ya'yan masarautar Kano, kuma mai sharhi kan harkokin masarauta, ya shaidawa Legit cewa tun can a kan samu dambarwa irin wannan.
Ya na ganin yadda yan siyasa ke siyasantar da lamuran masarautu a Najeriya ya saba doka, domin a cewarsa bai dace dan siyasa ya tashi rana guda ya rushe ko kirkiro masarauta ba.
Dr. Ibrahim Ado Kurawa ya ce:
"Maganar a ce kar yan siyasa su yi harkar sarauta bai taso ba, saboda su ma su na cikin al'umma. Amma kamata ya yi su yi hakan (shiga harkar masarautu) yadda ya dace da doka.
"Babu dalilin da zai sa wani mutumi kawai ya na zaune ya ce na kirkiri masarauta, musamman mu a kasar Hausa. Mu ba kasar Kudu ba ce, dama can muna da masarautun nan."
"To me yasa za a taba su? Abin da ya ke jawo rigima ke nan, kawai mutum idan ba ka son shi, sai ka zo ka ce ka cire shi ka nada wani."
Sarkin Kano na 16 ya yi nadin sarauta
A baya mun ruwaito cewa Sarkin Kano 16, Malam Muhammadu Sanusu II ya amince da nadin Alhaji Gambo a matsayin Jakadan Garbo duk da halin da ake ciki na rikicin masarauta.
Sabon nadin ya zo jim kadan bayan bayan Muhammadu Sanusi II ya amince da nadin Abba Yusuf wanda kawu ne ga Gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayin Dan Makwayon Kano.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng