'Ba Gadon Gidanku ba ne': PDP Ta Tsoma Baki kan Kiran Seyi Tinubu Ya Mulki Lagos

'Ba Gadon Gidanku ba ne': PDP Ta Tsoma Baki kan Kiran Seyi Tinubu Ya Mulki Lagos

  • Yayin da ake kiran dan Shugaba Bola Tinubu mai suna Seyi Tinubu ya tsaya takara, jam'iyyar PDP ta yi martani kan lamarin
  • Jam'iyyar reshen jihar Lagos ta soki masu tunzura Seyi neman takarar gwamnan jihar inda ta ce ba zai yiwu ba
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake cigaba da kiran Seyi Tinubu ya nemi takarar gwamna domin cigaba daga inda Sanwo-Olu ya tsaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Jam'iyyar PDP ta tsoma baki kan kiran dan Shugaba Bola Tinubu ya tsaya takarar gwamna a jihar Lagos.

Jam'iyyar reshen jihar ta koka kan kiraye-kirayen da ake yiwa Seyi Tinubu inda ta ce mulki fa ba gadon gidansu ba ne.

PDP ta yi fatali da kiran Seyi Tinubu ya nemi takarar gwamnan Lagos
Jam'iyyar PDP a Lagos ta ki amincewa da kiran Seyi Tinubu ya nemi takarar gwamna a jihar. Hoto: Seyi Tinubu, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: UGC

PDP ta soki Seyi Tinubu kan neman gwamna

Kara karanta wannan

Dalibai sun cire tsoro, sun fadawa Tinubu manyan matsaloli 2 da ke addabar Najeriya

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin jam'iyyar, Hakeem Amode ya fadawa jaridar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amode ya yi fatali da kiraye-kirayen inda ya ce Lagos ba za su taba goyawa mahaifinsa da kuma shi kansa Seyi Tinubu baya ba kan wannan abin da ake neman saka shi.

Ya caccaki masu neman mayar da mulkin Lagos ta iyalai inda ya ce hakan zai fuskanci turjiya mai tsanani daga wurinsu.

Tinubu: PDP ta fadi matsayar yan Lagos

"Muƙamin gwamnan Lagos ba kyauta ba ce, yan jihar sun riga sun nuna kin amincewarsu da mulkin iyalan Tinubu a zaben 2023 inda suka ki zabensa."

- Hakeem Amode

Amode ya ce yan Lagos sun nuna kiyayyarsu ga Tinubu a zaben 2023 domin haka ba za su goyi bayan dansa ba ko kadan, cewar Vanguard.

An soki 'ya'yan Tinubu kan halin kunci

Kun ji cewa Folashade Tinubu-Ojo ta roki mutanen Najeriya suyi hakuri da gwamnatin Bola Tinubu duk da wahalar da al’umma suke ciki.

Kara karanta wannan

Tura ta kai bango, matasan N Power za su fantsama tituna kan albashin watanni 9

Diyar shugaban kasar ta ce a sauran kasashen duniya, duk ana fuskantar irin abubuwan da ke faruwa a kasar nan a yanzu.

Shi ma Seyi Tinubu ya ce wajibi ne jama’a su jure kuncin da aka shiga muddin ana so a ji dadin rayuwa sosai a kasar nan gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.