An Kaure da Fada da Akpabio a Majalisa kan Fifita Sanatocin Arewa? Gaskiya Ta Fito
- Shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele ya mayar da martani kan jita-jitar rigimarsa da Godswill Akpabio
- Bamidele ya ce babu inda suka yi cacar-baki da ba hammata iska da shugaban Majalisar a ranar Laraba 20 ga watan Nuwambar 2024
- Hakan ya biyo bayan wallafa wani rahoto cewa Bamidele ya gwabza da Akpabio kan nunawa Sanatocin Kudu wariya a Majalisar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - An yi ta yada wasu rahotanni cewa an ba hammata iska tsakanin shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da Sanata Opeyemi Bamidele.
Sanata Bamidele ya yi martani kan jita-jitar inda ya ce labarin bai da asali, an yi ne domin jawo rigima a tsakaninsu.
An zargi rigima tsakanin Sanata Akpabio, Bamidele
Wani mai amfani da kafar X, Jackson Ude shi ya wallafa haka inda ya ce an gwabza tsakanin Bamidele da shugaban Majalisar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ude ya ce Bamidele ya zargi Akpabio da nuna wariya ga Sanatocin Kudu wurin ba da shugabancin manyan kwamitoci.
Rahoton ya ce Bamidele ya ce Akpabio na ba da manyan kwamitoci ga abokansa da ke Arewacin Najeriya inda da yake fifita su fiye da sanatocin Kudu.
Bamidele ya ƙaryata labarin rigima da Akpabio
Sai dai Sanata Bamidele ya yi watsi da lamarin a shafin Facebook inda ya ce wanda ya yada labarin ya saba batawa mutane suna.
Sanarwar ta ce babu gaskiya kan rigima tsakanin Akpabio da Sanata Bamidele a ranar Laraba 20 ga watan Nuwambar 2024.
Bamidele ya bukaci al'umma su yi watsi da jita-jitar inda ya ce an yi haka ne domin kawo sabani a tsakaninsu.
Akpabio ya yi bankwana da gawar sanata
Kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da shugaban Majalisa, Godswill Akpabio ya halarci bikin bankwana da gawar marigayi Sanata da ya rasu.
An kawo gawar Sanata Ifeanyi Ubah cikin Majalisar Dattawa domin sanatoci da sauran manyan mutane su yi masa bankwana a birnin Abuja.
Wannan na zuwa ne bayan mutuwar marigayi Sanata Ubah da ke wakiltar Anambra ta Kudu a Burtaniya a watan Yulin 2024 a cikin dakin otal.
Asali: Legit.ng