Yanzu Yanzu: An harbi tsohon dan majalisa, Opeyemi Bamidele a Ekiti

Yanzu Yanzu: An harbi tsohon dan majalisa, Opeyemi Bamidele a Ekiti

An harbi dan takarar gwamna a jihar Ekiti kuma mamba a majalisar wakilai na bakwai, Opeyemi Bamidele, tare da wani mutun daya.

A cewar Channels TV, an bayyana lamarin a matsayi wani hastarin harbi. Lamarin ya afku ne a ranar Juma’a, 1 ga watan Yuni a yayin gangamin dan takarar gwamna a jam’iyyar APC, Kayode Fayemi.

An tattaro cewa harsashin ya fito ne daga bindigar jami’in dan sanda wanda aka debo domin tabbatar da tsaro.

Yanzu Yanzu: An harbi tsohon dan majalisa, Opeyemi Bamidele a Ekiti
Yanzu Yanzu: An harbi tsohon dan majalisa, Opeyemi Bamidele a Ekiti

KU KARANTA KUMA: An kamo Zakuna biyu da damusa uku sun tsere daga Gidan Zoo a kasar Jamus

A wani rahoto daga jaridar The Punch an garzaya da Bamidele zuwa wani asibiti ba ba’a bayyana ba domin samun kulawar likita, yayinda aka ce mutun na biyun da ba’a gano ko wanene ba ya mutu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku bi shafukanmu domin samun labarai https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga hanyar mallakar sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel