"Alakar Wike da Tinubu Ba Ta Dame Mu Ba," Sanata Abba Ya Faɗi Abin da PDP Ta Sa a Gaba

"Alakar Wike da Tinubu Ba Ta Dame Mu Ba," Sanata Abba Ya Faɗi Abin da PDP Ta Sa a Gaba

  • Shugaban marasa rinjaye na majaisar dattawa, Sanata Abba Moro ya ce PDP ba ta damu da ɗasawar Wike da Shugaba Tinubu ba
  • Abba Moro ya ce babban abin da suka sa a gaba a yanzu shi ne yadda za su daso da PDP kan ganiyarta kuma su haɗa kai wuri ɗaya
  • Sanatan ya yi wannan bayani ne jim kaɗan bayan fitowa daga taron sanatocin PDP wanda ya gudana a Abuja ranar Laraba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Sanata Abba Moro mai wakiltar Benuwai ta Kudu a inuwar PDP ya ce ɗasawar Bola Tinubu da ministan Abuja, Nyesom Wike ba ta damu jam'iyyar ba.

Abba Moro, shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa ya ce a yanzu PDP ta fi maida hankali wajen lalubo hanyoyin warware rikicin da ya dabaibaye ta.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ba da umarnin rufe makarantu saboda mutuwar Sanata, bayanai sun fito

Sanata Abba Moro.
Sanata Abba Moro ya ce sun dukufa aikin lalubo hanyar warware rikicin PDP Hoto: @Imranmuhdz
Asali: Twitter

Sanatan ya faɗi hakan ne a daren Laraba da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan wani taron sirri na sanatocin PDP, Tribune Nigeria ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wike: Sanata Abba ya faɗi shirin PDP

Abba Moro ya ce a halin yanzu babu abinda ya fi ci wa jam'iyyar PDP tuwo a kwarya kamar rashin jituwar cikin gida da kuma taƙaddamar shugabanci.

Ya ce:

"PDP ba ta Damagum ko Wike ba ce, jam'iyyar PDP ta kowa ce, a yanzu mun duƙufa aiki don dawo da ita kan turbar nasara. Abin da Wike ya mana ba sabon abu ba ne."
"Abin da ya fi tsaya mana shi ne yadda za mu haɗa kai, mu zama tsintsiya ɗaya, duk wani abu da zai lalata mana zaman lafiyar jam'iyya mu jefar da shi."

Abin da sanatocin PDP suka tattauna a taro

Da yake ƙarin haske kan abin da suka tattauna a taron, Sanata Abba Moro ya ce sun duba zaben gwamnan da aka yi kwanan nan a jihohin Edo da Ondo.

Kara karanta wannan

"Tinubu ne babbar matsalarmu," Tsohon ɗan takarar gwamna ya soki shugaban ƙasa

Ya ce duk da sakamakon bai masu kyau ba amma sun yaba da kokarin PDP a zaɓukan da aka yi a jihohin guda biyu.

Sai dai Sanata Abba ya soki hukumar zaɓe watau INEC bisa abin da ya kira take dokokin zaɓe, inda ya nemi a sake garambawul domin dawo da ƙimar zaɓe a Najeriya.

'Tinubu ne babbar matsalar PDP'

A wani rahoton, an ji cewa tsohon ɗan takarar gwamna a jihar Ogun, Segun Sowunmi ya ɗora laifin rikicin da ke faruwa a PDP kan shugaban ƙasa, Bola Tinubu.

Sowunmi ya ce bai ga dalilin da Tinubu zai ɗauki tsohon gwamnan Ribas, Nyesom Wike ya naɗa shi minista ba tare da tuntuɓar PDP ba

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262