'Ɗa Zai Gaji Ubansa,' Ana So Ɗan Shugaba Tinubu Ya Tsaya Takarar Gwamnan Legas

'Ɗa Zai Gaji Ubansa,' Ana So Ɗan Shugaba Tinubu Ya Tsaya Takarar Gwamnan Legas

  • Da alama an fara kaɗa gangar takarar gwamna a jihar Legas duk da kwai sauran kusan shekaru uku kafin zaben
  • Gamayyar kungiyar matasan Najeriya ta fara kiraye-kirayen ɗan shugaban ƙasa, Seyi Tinubu ya tsaya takara
  • Ta bayyana yakinin Seyi Tinubu zai gaji mahaifinsa wajen zazzago ayyukan da za su daukaka jihar Legas kamar a baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos - Gamayyar kungiyar matasa ta 'Coalition of Nigerian Youth Leaders (CONYL)' ta fadi wanda ta ke so ya zama gwamnan Legas.

CONYL ta ce akwai buƙatar dan shugaban ƙasa, Bola Tinubu watau Seyi Tinubu ya nemi kujerar da babansa ya hau a kakar zabe ta 2027.

Tinubu
Matasa na son Seyi Tinubu ya tsaya takarar gwamnan Legas Hoto: Musuliu Akinsanya Ayinde/Asefon Sunday Dayo
Asali: Facebook

Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa ƙungiyoyin matasan da suka fito daga shiyyoyi shida na kasar nan sun bayyana dalilinsu na sha'awar Seyi Tinubu ya zama gwamnan Legas.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya aika saƙo ga majalisar dattawa kan sababbin naɗin da ya yi a INEC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matasa na son Seyi Tinubu ya yi gwamnan Legas

Matasan sun nemi Seyi Tinubu ya gaji mahaifinsa wajen zama gwamnan jihar Legas a zaben 2027 bayan gudanar da babban taronsu na ƙasa.

Hakan na ƙunshe a sanarwar haɗin gwiwa da shugaban ƙungiyar, Goodluck Ibem, Sakatare;Junard Abubakar, kakakinsu Iniobong Sampson da sakataren yaɗa labarai, Adeyemo Adewale.

Legas: Dalilin goyon bayan Seyi Tinubu a 2027

Gamayyar matasan Najeriya ta fadi abin da ya sa ta bukaci Seyi Tinubu ya tsaya takara domin zama gwamnan jihar Legas a 2027.

Kungiyar ta ce kyawawan ayyukan Bola Tinubu a lokacin da ya ke gwamna ya kawo gagarumin cigaba a Legas, kuma ta na kyautata zaton Seyi zai yi koyi da babansa.

Tinubu ya ɗauko tsohon kwamishinansa na Legas

A wani labarin kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya sake naɗa tsohon kwamishinansa da ya yi aiki da shi a Legas a babban muƙami a tarayya.

Kara karanta wannan

Gwamna ya cire tsoro, ya bayyana wasu 'ƴan siyasa' da ke ɗaukar nauyin ƴan bindiga

Shugaba Tinubu ya ɗauko Olatunji Bello, wanda ya riƙe muƙamin kwamishinan muhalli a karkashin gwamnoni da dama, ya naɗa shi a matsayin jami'in kula da hukumar FCCPC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.