Mace Tilo da Mataimakan Gwamna 11 da Suka Gaji Kujerar Iyayen Gidansu
A ranar Asabar 16 ga watan Nuwambar 2024 aka gudanar da zaben jihar Ondo inda Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya yi nasara.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya shiga jerin mataimakan gwamnoni da suka yi nasarar darewa kujerar gwamna a Najeriya.
Mataimakan gwamna da suka zama gwamnoni
Tribune ta fitar wani rahoto inda ta bayyana akalla tsofaffin mataimakan gwamna 12 da suka yi nasarar zama gwamnoni.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit Hausa ta binciko muku mataimakan gwamnan da suka gaji kujerar iyayen gidansu saboda mutuwa ko kuma tsige su da aka yi.
1. Goodluck Jonathan - Jihar Bayelsa
An zabi tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a matsayin mataimakin gwamna a shekarar 1999 karkashin Gwamna Diepreye Alamieyeseigha.
Jonathan ya rike mukamin har zuwa 2005 kafin rantsar da shi a matsayin gwamnan bayan Majalisar dokokin jihar ta tsige Alamieyeseigha.
Daga bisani, Jonathan ya zama mataimakin shugaban kasa a 2007 inda aka sake rantsar da shi a matsayin shugaban kasa a 2010 bayan mutuwar Umaru Musa Yar'Adua.
2. Patrick Yakowa - Jihar Kaduna
Marigayi Patrick Yakowa ya zama gwamnan Kaduna bayan daukar Gwamna Namadi Sambo a wancan lokaci a matsayin mataimakin Goodluck Jonathan a 2010, Pulse ta ruwaito.
Sai dai Yakowa ya rasa ransa a hatsarin jirgin sama a watan Disambar 2012 tare da mai ba Jonathan shawara a harkar tsaro, Andrew Azazi inda mataimakinsa Mukhtar Ramalan Yaro ya dare mulki.
3. Mukhtar Ramalan Yero - Jihar Kaduna
Bayan rasuwar marigayi Patrick Yakowa a 2012 a hatsarin jirign sama, mataimakinsa, Mukhtar Ramalan Yero ya gaji kujerarsa.
Ramalan Yero ya mulki jihar Kaduna daga shekarar 2012 zuwa 2015 inda aka yi zabe Nasir El-Rufai ya kwace mulki.
4. Bala James Ngilari - Jihar Adamawa
Bala Ngilari ya zama gwamnan jihar Adamawa a watan Oktoban 2014 bayan tsige mai gidansa, Murtala Nyako inda ya kammala wa'adin har shekarar 2015.
Nyako ya rasa kujerarsa ne bayan mambobin Majalisar jihar sun tsige kan zargin badakalar makudan kudi.
5. Ibrahim Geidam - Jihar Yobe
Ibrahim Geidam ya dare kujerar mulkin jihar Yobe bayan rasuwar Gwamna Mamman Bello Ali a watan Janairun 2009.
Geidam ya rike mukamin mataimakin Bello Aliyu daga 2007 zuwa 2009, daga bisani ya tsaya takarar inda ya lashe zabukan 2011 da kuma 2015 a jihar.
6. Abdullahi Ganduje - Jihar Kano
Shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje ya rike mukamin mataimakin Rabiu Kwankwaso daga 1999 zuwa 2003 da kuma 2011 zuwa 2015.
Daga bisani, Ganduje ya gaji kujerar Kwanwkaso a 2015 karkashin APC kafin sake nasara a karo na biyu a 2019.
A halin yanzu, Ganduje da tsohon mai gidansa ba su ga maciji da juna wanda ya yi matukar tasiri a siyasar jihar Kano.
7. Umar Namadi - Jihar Jigawa
Gwamna Umar Namadi ya gaji kujerar gwamnan jihar Jigawa daga mai gidansa Badaru Abubakar wanda yanzu ke rike da Ministan tsaro.
Namadi ya rike mukamin mataimakin Badaru daga shekarar 2019 zuwa 2023 karkashin jam'iyyar APC.
8. Mahmud Shinkafi - Jihar Zamfara
Mahmud Shinkafi ya samu nasarar zama gwamnan Zamfara bayan ya gaji kujerar Sanata Ahmad ani Yerima a 2007.
Shinkafi ya dare kujerar a karkashin ANPP kafin daga bisani ya koma PDP a 2008 kuma ya rasa damar dawowa kujerar a karo na biyu a 2011.
9. Lucky Aiyedatiwa - Jihar Ondo
Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya zama gwamnan jihar a watan Disambar 2023 bayan mutuwar Rotimi Akeredolu.
Aiyedatiwa ya nemi takara a zaben Nuwambar 2024 da aka yi inda ya lashe zaben karkashin APC.
10. Dave Umahi - Jihar Ebonyi
A shekarar 2011, Dave Umahi ya zama mataimakin gwamnan karkashin Gwamna Martin Elechi a jihar Ebonyi.
Umahi wanda yanzu ke rike da mukamin Ministan ayyuka ya dare kujerar gwamna a 2015 karkashin PDP kafin daga bisani ya koma APC.
11. Virginia Etiaba - Jihar Anambra
Etiaba ta kafa tarihi da ta rike mukamin mataimakiyar gwamna ta farko da ta zama gwamnan jihar a 2006 bayan tsige Peter Obi.
Sai dai ba ta dade a kan kujerar ba yayin da ta dawo da mulki ga Obi bayan watanni uku da aka bayyana tsigewar a matsayin haramtacciya.
12. Adebayo Alo-Akala- Jihar Oyo
An zabi Alao-Akala a matsayin mataimakin gwamna karkashin Gwamna Rashid Ladoja a 2003 bayan tsige shi da Majalisa ta yi.
Alo-Akala ya shafe shekaru uku ne a matsayin mataimaki daga 2003 zuwa 2006 yayin da aka dawo da Ladoja a 2006, Alao- Akala ya zama gwamnan jihar a zaben 2007 da aka gudanar.
Mataimakan gwamna mata a Najeriya da jihohinsu
A baya, kun ji cewa mata sun farga sun daina sanya a harkokin siyasa a ƙasar nan, inda yanzu suke fitowa su shiga a dama da su a cikin harkokin siyasa.
Mata da dama sun riƙe muƙaman siyasa tun daga matakin kansila har ya zuwa na mataimakiyar gwamna.
Asali: Legit.ng