An saki tsohon Gwamnan Adamawa bayan hukuncin daurin shekaru 5

An saki tsohon Gwamnan Adamawa bayan hukuncin daurin shekaru 5

- Justice Nathan Musa,ne ya bada umurnin daure tsohon gwamnan jihar Adamawa Mr Bala James Ngilari, na tsawon shekaru biyar, kuma shine ya bada belinsa bisa dalilan rashin lafiya

- A zaman kotun da ya cika da magoya bayan tsohon gwamnan, babban lauyan Najeriya Sam Olugunorisa, (SAN) ya shaidawa kotun cewa tun bayan kai shi jarun, lafiyar tsohon gwamnan ke kara tabarbarewa wanda a dalilin haka ne suka bukaci a bashi beli domin ya je a duba lafiyarsa

An saki tsohon Gwamnan Adamawa bayan hukuncin daurin shekaru 5
Tsohon Gwamnan Adamawa

Haka nan ma kuma Legit.ng ta samu labarin cewa a zaman kotun an mika wata wasikar da hukumar kula da gidajen yari a jihar suka rubuta game da tabarbarewar lafiyar tsohon gwamnan Bala Ngillari, inda a wasikar dake dauke da sa hannun mataimakin kwanturolan gidajen yarin jihar Adamawan, Mr John Bukar ya rattabawa hannu, an bayyana cewa hawan jinin tsohon gwamnan jihar Adamawan ya karu zuwa 200 daga 100 yayin da ciwon sugarsa kuma ya karu zuwa 160.

Magoya bayan tsohon gwamnan irinsu Hon Abdullahi Prembe, tsohon kwamishinan yada labarai a zamanin Ngillarin, ya bayyana farin cikinsu da cewa zasu cigaba da neman hakkinsu.

KU KARANTA: Babban bankin Najeriya ya sanar da sabon farashin Dala

Ita ma jam’iyar PDP, ta yaba da matakin bada belin da kotun ta yi, kamar yadda Barr.A.T Shehu, sakataren wani bangare na jam’iyar PDP a jihar yace suna farin ciki.

A ranar Litinin shida ga wannan wata na maris ne tsohon Gwamnan jihar Adamawan James Bala Ingilari, ya zamo tsohon gwamna na biyu a tarihi da aka daure kan aikata laifukan da suka shafi cin hanci da rashawa.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa

Da Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli yadda mutanen Daura suka yi murnanr dawowar Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel