Kai Tsaye: Yadda Zaben Gwamnan Ke Gudana a Jihar Ondo, APC da PDP Sun Ja Daga
Rana ba ta ƙarya, a yau Asabar, 16 ga watan Nuwamba, 2024 ne al'ummar jihar Ondo za su zaɓi sabon gwamnan da zai jagorance su na tsawon shekaru huɗu.
A bayanan hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC, ƴan takara 18 ne suka shirya fafatawa a zaben karƙashin iniwar jam'iyyu daban-daban.
Daga cikinsu akwai Gwamna Lucky Aiyedatiwa na APC da kuma tsohon mataimakin gwamna, Agboola Ajayi, wanda ke takara a inuwar PDP.
Legit Hausa ta shirya tsaf kuma wakilanmu sun kimtsa sun yi karin kumallo domin kawo maku abubuwan da ke faruwa kai tsaye daga jihar Ondo.
Kayan zabe sun isa mazabar ɗan takarar PDP
Malaman zaɓe na wucin gadi sun isa mahaifar ɗan takarar gwamna a inuwar PDP tare da kayan zaɓe a kan lokaci yayin da zaɓe ya kankama a Ondo.
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa da karfe 6:50 na safe, ma’aikatan wucin gadi na INEC tare da rakiyar jami’an tsaro sun isa rumfar zaben da ɗan takarar PDP ke kaɗa kuri'a.
Agboola Ajayi na jam'iyyar PDP na kaɗa kuri'a ne a rumfar zaɓe da ke Kiribo, ƙaramar hukumar Ese-Odo.
Haka nan a rumfar zaɓe ta 5, da ke makarantar C. M a gunduma ta 2 a Kiribo, jami’an zabe sun iso da misalin karfe 7 na safe.
Gwamnan Ondo ya kada kuri’arsa
Gwamna Lucky Aiyedatiwa, na jihar Ondo ya kada kuri’asa a zaben da ya ke neman jama’a su mayar da shi kan kujerar da ya ke kai.
Gwamnan, wanda ke sake neman kujerar gwamna a karkashin jam’iyyarsa ta APC, ya kada kuri’arsa a safiyar nan.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa ya sanya kuri’arsa a akwati mai lamba biyar, mazaba ta hudu da ke yankin Obenla na karamar hukumar Ilaje.
Lucky Aiyedatiwa ya yaba da kyakkyawan shirin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta yi wajen gudanar da zaben.
DJ na nishandantar da yan mazabar gwamna Aiyedatiwa
Masu shirin kada kuri’a a mazabar gwamna Lucky Aiyedatiwa su na nishadantuwa bayan an gayyato DJ zuwa wurin.
Lamarin ya afku a mazaba ta hudu da ke yankin Obenla a karamar hukumar Ilaje, inda ake sa ran gwamna Aiyedatiwa zai kada kuri’arsa anjima.
Gwamnan, wanda ya fito daga jam’iyyar APC ya na daga cikin masu neman kujerar da ya ke kai a yanzu, kamar yadda The Cable ta wallafa.
Jami'an INEC sun isa Ondo ta Arewa
Da misalin ƙarfe 7.10 n.s jami'an hukumar zabe (INEC) su ka isa mazaba ta 8, rumfar zabe ta 25 a Ondo ta Arewa, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Zuwa yanzu sun shirya domin fara tantance jama'a don zaben gwamnan da zai jagoranci jihar na shekaru huɗu masu zuwa.
Manyan ƴan takara 3 a zaɓen Ondo
Lucky Aiyedatiwa - APC
Agboola Ajayi - PDP
Ayodele Festus Olorunfemi - LP
Zaben Ondo: Bayanan da ya kamata ku sani
Masu rijistar zaɓe - 2,053, 061
Adadin kananan hukumomi - 18
Adadin gundumomi - 203
Adadin rumfunan zabe - 3,933
Adadin waɗanda suka karɓi katin zaɓe - 1,757,205
Adadin katin zaɓen da ba a karɓa ba - 295,856.
Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262
Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.