Yadda Bwala Ya Bar APC, Ya Shiga PDP, Ya Lallaba Ya Dawo Aka ba Shi Mukami
- Asali Daniel Bwala ya na cikin ‘ya ‘yan jam’iyyar APC sai aka ji ya fice saboda an tsaida musulmi da musulmi takara
- Daga nan ne sai ya koma PDP kuma ya marawa Atiku Abubakar/Ifeanyi Okowa baya, amma suka fadi zaben 2023
- Bayan nasarar Bola Tinubu sai Bwala ya sake dawowa, yanzu ya lashe duk amansa, ya samu mukami a Aso Villa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Sanata Ovie Omo-Agege ya nada Daniel Bwala a matsayin mai taimaka masa wajen harkokin shari’a da kundin tsarin mulki.
Kafin zama hadimin mataimakin shugaban majalisar dattawan, Daniel Bwala ya yi karatun shari’a a jami’o’in Najeriya da kasar waje.
Rahoton nan ya kawo yadda Bwala ya rika yawo tsakanin jam’iyyu, ya na canza gida kafin zama hadimin shugaban kasa na sadarwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daniel Bwala a jam’iyyar APC
Bayan Sanata Ovie Omo-Agege ya zama mataimakin shugaban majalisar dattawa sai a nada Daniel Bwala a cikin masu taimaka masa.
A lokacin har ana cewa Bwala shi ne mai ba APC shawara a kan harkokin shari’a, zargin da uwar jam’iyya ta karyata ta bakin Felix Morka.
Yadda Bwala ya fice daga APC
A lokacin da za a yi zaben 2023, Bola Tinubu ya dauki Kashim Shettima a matsayin abokin gami, sai aka rahoto cewa Bwala ya bar APC.
Tashar Arise TV ta ce lauyan ya fice daga APC ne saboda ba zai goyi bayan tikitin musulmi da musulmi a zaben shugaban Najeriya ba.
PDP ta shiga zawarcin Bwala
Daily Post ta kawo yadda wasu ‘yan PDP a majalisar tarayya suka ziyarci Bwala, suka yi kokarin shigo da shi cikin jam’iyyar a Yulin 2022.
Hon. Ndudi Elumelu ya roki ‘dan siyasar ya bi jirgin Atiku Abubakar a zaben 2023, kuma a karshe ya amsa wannan kira da aka yi masa.
Kusan wata guda bayan barin APC, Punch ta ce Bwala ya shiga PDP kuma aka nada shi cikin masu magana da yawun Atiku Abubakar.
A wata hira da aka yi da shi, ‘dan siyasar ya karyata zargin da ake yi masa na barin jam’iyyarsa domin ya samu mukami wajen Atiku.
Lokacin ne ya fadawa duniya cewa da ya yi zamansa a APC, mukami ya na jiransa daga Tinubu wanda a karshe ya lashe zaben 2023.
Ziyartar Tinubu a Aso Villa
A karshe dai Atiku Abubakar ya sha kashi a zaben 2023, Bwala ya ce an yi murdiya. An gama wannan kenan sai aka gan shi a Aso Villa.
Daga nan sai aka ji ya fara yabawa shugaba Bola Tinubu, tun daga nan irinsu Segun Sowonmi suka gane cewa zai sake sauya sheka.
Ganin haka wasu suka fara cewa shugaban kasa zai ba shi mukami musamman bayan tafiyar Cif Ajuri Ngalele, kuma hakan aka yi.
Shugaba Tinubu ya tuna da Bwala
Ana da labari Bola Tinubu ya nada Daniel Bwala a matsayin mai taimakasa masa a fadar Aso Rock a harkokin sadarwa da yada labarai.
Bwala lauya, masanin shari’a ne kuma malami wanda ake ganin bai da amana a siyasa, nadin na shi ya jawo surutu a makon nan.
Asali: Legit.ng