Zaben Ondo 2024: Muhimman Abubuwa Dangane 'Yan Takara 4 a APC, PDP, SDP da LP
- Mutanen jihar Ondo za su fito su zaɓi gwamnan da zai jagorance nan da shekara huɗu masu zuwa a ranar Asabar
- Manyan ƴan takara huɗu na jam'iyyun APC, PDP, SDP da Labour Party ne kan gaba a zaɓen da ake shirin gudanarwa
- Kowanne daga cikin ƴan takarar akwai rawar da ya taka kafin ya kai ga matsayin neman kujerar gwamna a zaben
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Ondo - Ana ta shirye-shiryen gudanar da zaɓen gwamna a jihar Ondo a ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamban 2024.
Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jam'iyyar APC da Agboola Alfred Ajayi na PDP na daga cikin manyan ƴan takarar da ake tunanin za su iya yin nasara a zaɓen.
Abubuwan sani dangane da ƴan takarar gwamnan Ondo
Legit Hausa ta tattaro muhimman abubuwan sani dangane da manyan ƴan takarar gwamnan Ondo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Lucky Orimisan Aiyedatiwa (APC)
An haifi Lucky Orimisan Aiyedatiwa a ranar, 12 ga watan Janairun 1965 a garin Obe-Nla cikin ƙaramar hukumar Ilaje ta jihar Ondo, cewar rahoton BBC.
Lucky Aiyedatiwa ya samu satifiket ɗin NCE a fannin tattalin arziƙi da gwamnati daga kwalejin ilmi ta jihar Legas (da yanzu ta koma jami'ar ilmi ta jihar Legas) a shekarar 1986.
Ya zama mataimakin gwamnan jihar Ondo a watan Oktoban 2020 bayan sun yi nasara da shi da marigayi Gwamna Rotimi Akeredolu.
Bayan ya zama mataimakin gwamna, daga baya ya zama gwamna na riƙon ƙwarya lokacin da Akeredolu ya tafi jinya a ƙasar waje.
An rantsar da shi a matsayin gwamnan jihar Ondo a watan Disamban 2023, bayan rasuwar Gwamna Rotimi Akeredolu.
2. Agboola Alfred Ajayi (PDP)
Agboola Alfred Ajayi mai shekara 54 shi ne ɗan takarar jam'iyyar PDP a zaɓen gwamnan jihar Ondo na shekarar 2024.
An haifi Agboola Alfred Ajayi a ranar, 24 ga watan Satumban 1968 a Ondo, cewar rahoton BBC Pidgin.
Ya yi karatunsa na firamare da sakandire a jihar Ondo kafin daga bisani ya samu kwalin digiri a fannin shari'a daga jami'ar Igbinedion da ke Okada a jihar Ondo.
Ya yi wa marigayi Gwamna Rotimi Akeredolu mataimakin gwamna a wa'adin mulkinsa na farko.
Agboola Alfred Ajayi ya taɓa riƙe muƙamin shugaban jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) a shekarar 1988.
Ya taɓa zama shugaban ƙaramar hukumar Ese-Odo a jihar Ondo a shekarar 2004.
3. Otunba Bamidele Akingboye
Otunba Bamidele Akingboye shi ne ɗan takarar jam'iyyar SDP a zaɓen gwamnan jihar Ondo na shekarar 2024.
Akingboye haifaffen garin Okitipupa ne wanda nan ne hedkwatar ƙaramar hukumar Okitipupa ta jihar Ondo.
Ya halarci manyan makarantu da suka haɗa makarantar kasuwanci ta Legas (Jami'ar Pan-Atlantic), jami'ar Heriot-Watt da ke Edinburgh, a ƙasar Scotland da makarantar kasuwanci ta Harvard.
4. Sola Ebiseni (LP)
Sola Ebiseni shi ne ɗan takarar gwamnan jihar Ondo na jam'iyyar Labour Party a zaɓen 2024.
An haife shi a ranar, 1 ga watan Oktoban 1960 a jihar Ogun amma iyayensa ƴan asalin garin Ilaje ne a jihar Ondo.
Ya taɓa riƙe muƙamin kwamishina a gwamnatin Olusegun Mimiko wanda ya yi shekaru takwas a jere ya na mulki.
Jiga-jigan APC sun dura jihar Ondo
A wani labarin kuma, kun ji cewa jiga-jigan APC sun dura jihar Ondo yayin da ake shirin gudanar da zaben gwamna a ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamban 2024.
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya buƙaci mutanen Ondo su zaɓi jam'iyyar APC saboda ci gaban da shugaba Bola Tinubu ya kawo musu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng