A Karshe, Shugaba Tinubu Ya Sakawa Tsohon Hadimin Atiku da Mukami a Gwamnatinsa

A Karshe, Shugaba Tinubu Ya Sakawa Tsohon Hadimin Atiku da Mukami a Gwamnatinsa

  • Bayan dogon jira, Daniel Bwala ya samu muƙami a gwamnatin Bola Tinubu a yau Alhamis 14 ga watan Nuwambar 2024
  • Shugaba Tinubu ya amince da nadin Bwala a matsayin hadiminsa na musamman a bangaren sadarwa da hulda da jama'a
  • Wannan na zuwa ne bayan shafe watanni Bwala na yabon gwamnatin Tinubu, bayan ya yi watsi da Atiku Abubakar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya amince na nadin Daniel Bwala a matsayin hadiminsa na musamman.

Bola Tinubu ya ba Bwala muƙamin hadiminsa a bangaren sadarwa a fadar shugaban kasa.

Tinubu ya nada tsohon yaron Atiku mukami a gwamnatinsa
Bola Tinubu ya ba Daniel Bwala muƙamin hadimi na musamman. Hoto: @BwalaDaniel.
Asali: Twitter

Daniel Bwala ya bar Atiku da PDP

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin Tinubu a bangaren yada labarai, Dada Olusegun ya fitar a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya shiga ganawa da ministoci da manyan ƙusoshin gwamnati a Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon hadimin Atiku ya yi aiki tare da shi daga 2022 zuwa zaben 2023 da mai gidan nasa ya yi rashin nasara a hannun Tinubu.

Bwala ya tayar da kura bayan dawowa bangaren Bola Tinubu da ya lashe zabe da aka gudanar a 2023.

Hakan ya jawo maganganu da ake ta sukar Bwala da cewa ya zama butulu duba da yadda suka yi aiki tare da tsohon mataimakin shugaban kasar.

Tinubu ya nada sababbin shugabanni a gwamnati

Dada Olusegun a cikin sanarwar, ya kuma tabbatar da nadin sababbin shugabanni a hukumomi daban-daban a Najeriya.

Shugabannin sun hada da Mr. Olawale Olopade, shugaban hukumar wasanni ta kasa (NSC) da Dakta Abisoye Fagade, shugaban hukumar kula da baki da yawon bude ido a Najeriya.

Sannan na ukunsu shi ne Dakta Adebowale Adedokun, shugaban hukumar da ke sa ido a harkokin saye-saye na gwamnati (BPP).

Bwala ya fice daga PDP zuwa APC

Kara karanta wannan

EFCC: 'Yadda wani gwamna a Najeriya ya tura miliyoyin Naira zuwa asusun ɗan canji'

A baya, mun ba ku labarin cewa Daniel Bwala, tsohon mai magana da yawun kwamitin kamfen Atiku Abubakar ya bar jam'iyyar PDP.

Bwala ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan ganawa da shugaban ƙasa Bola Tinubu a Aso Villa, ya sanar da komawa jam'iyyar APC.

Ya kara jaddada goyon bayansa ga gwamnatin Tinubu, inda ya ce nan ba da jimawa ba zai tabbatar da komawa gida watau APC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.