Ganduje Ya Yi Illa, Ya Karɓi Sababbin Tuba, Ya Raba PDP da Tsohon Kwamishina
- Jam'iyyar APC karkashin jagorancin Abdullahi Ganduje ta sake samun karuwa na tsohon kwamishina kuma kusa a PDP
- Tsohon kwamishina a jihar Ebonyi, Abia Onyike ya tattara kayansa daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulki a Najeriya
- Kafin zama kwamishina a mulkin tsohon gwamna, Martin Elechi, Onyike ya rike muƙamin hadimi a gwamnatin Sam Egwu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ebonyi - Tsohon kwamishinan a jihar Ebonyi ya watsar da jam'iyyarsa ta PDP zuwa APC.
Jigon PDP, Abia Onyike ya yanke shawarar barin jam'iyyar PDP ne domin kama layin Abdullahi Ganduje.
Tsohon kwamishina ya bar PDP zuwa APC
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ya fitar, Onyike ya ce ya koma APC ne saboda ayyukan alheri na Gwamna Francis Ogbonna Nwifuru ke yi, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Onyike ya rike muƙamin hadimin tsohon gwamna, Sam Egwu kafin zama kwamishina a gwamnatin Martin Elechi.
'Dan siyasar ya tabbatar da ficewarsa daga PDP a taron siyasa a gundumar Owutu Edda da ke karamar hukumar Edda a jiya Laraba.
"Na yanke shawarar komawa APC ne saboda ayyukan alheri da Gwamna Francis Nwifuru ke yi a Ebonyi."
"Hakan zai taimaka wurin kara alaƙa mai ƙarfi domin ba Gwamna Nwifuru goyon baya kan inganta jihar da take yi."
- Abia Onyike
APC ta yi godiya da samun jigon PDP
Shugaban jam'iyyar APC a gundumar Owutu Edda, Mr. Oko Ogbuagu ya nuna farin cikinsa kan samun jigo kaman Onyike a tafiyarsu.
Ogbuagu ya ce za su rike Onyike hannu bibbiyu kamar asalin dan jam'iyyar ba tare da nuna wariya ba.
"An dade da gwada Onyike, dan siyasa ne mai jama'a, tabbas zuwansa APC zai yi matukar taimakawa a zabuka masu zuwa."
- Mr. Oko Ogbuagu
Gwamna ya karawa ma'aikata albashi
Kun ji cewa yayin da ake fama da tashin farashin fetur, gwamnan jihar Ebonyi ya amince da fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000.
Gwamna Francis Nwifuru ya yi bayanin cewa sabon albashin ba yana nufin kowane ma'aikaci zai samu ƙarin N70,000 a albashinsa ba ne.
Nwifuru ya ba da tabbacin cewa a shirye yake ya yi biyayya ga hukuncin kotun ƙolin Najeriya na ƴantar da ƙananan hukumomin jihohi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng