Ana Daf da Zabe, Yan APC Sun Watsawa Gwamna Kasa a Ido, Sun Goyi bayan Dan Adawa

Ana Daf da Zabe, Yan APC Sun Watsawa Gwamna Kasa a Ido, Sun Goyi bayan Dan Adawa

  • An samu rarrabuwan kawuna a jihar Ondo yayin da ake shirye-shiryen zaben da za a gudanar a makon gobe
  • Kungiyar matasan APC a jihar ta yi watsi dan takararta kuma Gwamna Lucky Aiyedatiwa a zaben da za a gudanar
  • Kungiyar mai suna Ondo Patriots ta nuna goyon bayanta ga dan takarar SDP a jihar, Benson Akingboye saboda wasu dalilai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ondo - Kungiyar matasan APC a jihar Ondo ta yi watsi da Gwamna Lucky Aiyedatiwa ana daf da zaɓe.

Kungiyar da ake kira Ondo Patriots ta nuna goyon bayanta ga dan takarar SDP a zaben gwamna, Benson Akingboye.

Kara karanta wannan

'Za mu gyara Najeriya,' Bukola Saraki ya fadi shirin da PDP ta yi na karbar mulki a 2027

Yan APC sun goyi bayan dan takarar SDP, sun yi watsi da Aiyedatiwa
Kungiyar matasan APC ta yi fatali da takarar dan jam'iyyarta, ta goyi bayan dan SDP a zaɓen gwamna. Hoto: Ondo APC Solidarity Group, Lucky Aiyedatiwa.
Asali: UGC

Ondo: Yan APC sun yi korafi ga Ganduje

Punch ta ruwaito cewa kungiyar ta yi farali dan takarar APC kuma gwamnan jihar, Lucky Aiyedatiwa ana saura mako daya zaɓe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na kunshe ne a cikin wani korafi da kungiyar ta rubuta ga shugaban APC, Abdullahi Ganduje a jiya Asabar.

Shugaban kungiyar, Dele Oyewo ya caccaki tsarin yadda aka gudanar da zaben fitar da gwani da ya samar da Aiyedatiwa, The Guardian ta ruwaito.

"Sun gwammace su zabi abin da zai faranta musu rai madadin abin da zai biyo bayan rashin yin adalci da suka yi."
"An tafka kuskure kan zaben Lucky Aiyedatiwa a matsayin wanda zai yi takara a zaɓen jihar Ondo."
"Hakan ya nuna ba mu da maraba da PDP a 2015, duba da kwarewar yan takara, mun yi yanke shawarar goyon bayan Benson Akingboye a SDP."

Kara karanta wannan

Kwanaki 9 kafin zaɓe, kotu ta raba gardama kan sahihancin dan takarar NNPP

- Ondo Patriots

Kotu ta dan takarar NNPP damar tsayawa

Kun ji cewa Yayin da ake shari'a game da sahihancin dan takarar gwamnan Ondo a NNPP, kotu ta raba gardama kan sahihancin dan takarar.

Kotun ta yi fatali da masu kalubalantar takarar Olugbenga Edema kan zargin cewa ba dan jam'iyya ba ne tun farko a zaben fitar da gwani.

Wannan na zuwa ne yayin da ake ta shirye-shiryen gudanar da zaben gwamna a Ondo a ranar 16 ga watan Nuwambar 2024 da muke ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.