Hukumar EFCC Ta Shirya Kama Wani Gwamnan PDP a Najeriya, Bayanai Sun Fito
- Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziki zagon ƙasa watau EFCC na shirin damke Gwamna Godwin Obaseki a mako mai zuwa
- Gwamna Obaseki ne ya yi wannan zargin, ya ce ya samu labarin za a kama shi bayan ya miƙa mulki ranar 14 ga watan Nuwamba
- A cewarsa ba ya tsoron jami'an hukumar EFCC ta kama shi kuma ya gama shirin amfani da wannan damar wajen bincike da karatu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Edo - Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya ce ya samu labarin hukumar yaƙi da rashawa watau EFCC na shirin cafke shi bayan ya miƙa mulki a makon gobe.
Gwamna Godwin Obaseki ya bayyana hakan ne a taron EdoBEST na kasa wanda ya gudana a Abuja ranar Alhamis.
Jaridar Leadership ta tattaro cewa a ranar 14 ga watan Nuwamba, 2024, Gwamna Obaseki zai miƙa mulki ga zababben gwamnan jihar Edo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
EFCC na shirin kama Gwamna Obaseki?
Da yake jawabi a wurin taron, gwamnan ya ce labari ya zo kunnensa cewa da zarar ya miƙa mulki jami'an EFCC za su yi ram da shi.
Godwin Obaseki ya ce a bayanan da ya samu, EFCC na shirin cafke shi kan zargin zamba da karkatar da kudin talakawa a zamanin mulkinsa, Tribune ta rahoto.
Sai dai a cewarsa ba ya tsoron binciken EFCC, yana mai ƙarawa da cewa idan an tsare shi zai amfani da wannan damar wajen karatun litattafai da bincike.
EFCC: Obaseki ya faɗi matakin da zai ɗauka
"Na ji labarin EFCC za ta kama ni mako mai zuwa bayan karewar wa'adina, duk inda suka kai ni suka tsare zan yi amfani da damar na kara nazari da bincike."
"Mun yi ayyuka da yawa waɗanda za a tuna mu da su, na yi imanin ɗaya daga cikin abubuwan da muka fi maida hankali shi ne batun jama'a da duk abin da ya dame su."
"To me zan ji tsoro? Na maida hankali ne kawai ga abin da na yi imani da shi, kuma a yau, kuna iya ganin abin da muka cimma, duk abin da ya biyo baya kuma ba yadda muka iya."
- Godwin Obaseki.
Gwamnan Edo ya gamsu ya ayyukansa
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan Edo mai barin gado, Godwin Obaseki na ci gaba da buɗe ayyukan da ya kammala yayin da yake shirin miƙa mulki.
Obaseki ya bayyana cewa ya gamsu da ayyukan da ya yi wa al'umma a mulkinsa, ya ce ya cika alƙawurran da ya ɗauka lokacin yake yakin neman zabe.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng