"Ban faɗi zaɓen 2023 ba," Atiku Ya Fallasa Yadda Tinubu Ya Masa Karfa Ƙarfa
- Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya ce shi ne ya lashe zaben 2023 amma aka murde zaben karfi da yaji
- Atiku ya jaddada cewa bai fadi zaben 2023 ba, yana mai cewa su ma masu kada kuri'a sun gane cewa ba wanda suka zaba aka basu ba
- Game da matsin tattalin arziki da ake fama da shi, Atiku ya ce shugaba Bola Tinubu ya hau mulki ba tare da wani tsari mai kyau ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a 2023, Atiku Abubakar ya ce bai fadi zaben shugaban kasar da aka gudanar a bara ba.
Atiku Abubakar ya yi ikirarin cewa ta karfi da yaji ne aka 'sace' nasarar zabensa, wanda hakan ke nufin matsayarsa kan cewa shi ne ya lashe zaben.
Atiku Abubakar ya ce bai fadi zaben 2023 ba
A wasu jerin gwanon sakonni da ya aika a shafinsa na X a ranar Litinin, Atiku ya yi ikirarin cewa an yi masa fashin nasarar zaben da ya samu a 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku ya bayyana cewa:
"Bari in jaddada cewa ‘yan kasar da suka kada kuri’unsu a zaben shugaban kasa na 2023 suna sane da cewa ban fadi zaben ba.
"Mawuyacin halin da muka tsinci kanmu a yau ya faru ne sakamakon fashin kuri'un da aka yi mana a zaben, aka canza zabin al'umma."
Atiku ya caccaki gwamnatin Tinubu
Atiku ya zargi shugaba Bola Tinubu da haddasa tsadar rayuwar da 'yan Najeriya ke ciki, saboda aiwatar da "tsare-tsaren tattali masu cike da kura-kurai."
Ya koka da cewa a halin yanzu 'yan Najeriya na cikin "rikicin tattalin arziki," saboda shugaban kasa ya hau kan karagar mulki ba tare da wani "tsari mai bullewa ba."
A sakon da ya wallafa, tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa:
"Na yi imani da cewa mun tsinci kanmu a cikin wannan tabarbarewar tattalin arziki ne sakamakon yadda gwamnatin Tinubu ta hau mulki ba tare da wani tsari mai kyau ba."
Gwamnatin Tinubu ta soki kalaman Atiku
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi martani bayan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya soki tsare-tsaren gwamnatin.
Gwamnatin ta ce babu dalilin da zai sa Atiku Abubakar ya rika kwatanta matakan gwamnati da kudurinsa wanda babu wanda ya taba gwada su ballatana a gano amfaninsu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng