'Halinsa ne': Musa Kwankwaso Ya Fadi Silar Watsewa Jagoran Kwankwasiyya a Kano
- Jigon jam'iyyar APC a jihar Kano, Musa Ilyasu Kwankwaso ya magantu kan yadda rigimar Kwankwasiyya ke kara kamari
- Ilyasu Kwankwaso ya nuna damuwa kan yadda aka yi watsi da Baffa Bichi duk da gudunmawar da ya ba tafiyar tun farko
- Tsohon kwamishinan ya ce abin dubawa ne yadda duk wanda ke tare da Sanata Rabi'u Kwankwaso sai ya gudu ya bar shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Tsohon kwamishina a jihar Kano, Musa Ilyasu Kwankwaso ya yi magana kan rigimar Kwankwasiyya.
Ilyasu Kwankwaso ya ce abin takaici ne yadda kowa ya zo wurin Sanata Rabi'u Kwankwaso sai ya gudu da ƙafarsa.
Kwankwasiyya: Musa Ilyasu Kwankwaso ya fasa kwai
Tsohon kwamishinan ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da Mu'az Magaji ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin faifan bidiyon, Ilyasu Kwankwaso ya bayyana yadda ya kasance daga cikin wadanda suke tare da Sanata Kwankwaso tun farko.
Ya ce amma abin takaici duk taron jama'ar Kwankwaso a wancan lokaci da yawansu sun gudu sun bar shi, ya ce ba abin kirki yake kullawa ba.
Musa Kwankwaso ya fadi gudunmawarsa a Kwankwasiyya
"Ni Musa Ilyasu Kwankwaso duk wadanda suke gindinsa sun sani da ni aka fara, duk wadanda suke wurin kadan ne aka fara da su."
"Kowa yanzu ya gudu, su Bello Hayatu da Nasiru Ali Koki sun gudu, ga su nan birjik su Bakwana da Bala Gwagwarwa duk sun gudu."
"Duk wadannan mutanen su gudu, anya Kwankwaso abin kirki yake yi kuwa kowa ya zo sai ya gudu?"
- Musa Ilyasu Kwankwaso
Ilyasu Kwankwaso ya ce ai yanzu Jagora yana cikin tashin hankali saboda alhaki ya kama shi ba zai iya magana ba.
Yan Majalisar Tarayya 2 sun bar NNPP
Kun ji cewa tafiyar Kwankwasiyya ƙarƙashin jagorancin Rabiu Musa Kwankwaso ta samu koma baya a jihar Kano.
Wasu ƴan majalisar wakilai guda biyu na jam'iyyar NNPP sun sanar da ficewarsu daga tafiyar Kwankwasiyya.
Ɗaya daga cikinsu ya bayyana cewa tafiyar Kwankwasiyya babu komai a cikinta face ƙarya, cin amana da yaudara.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng