Abba Ya Daina Ɗaga Wayar Kwankwaso, Rikicin NNPP Ya yi Ƙamari
- Rahotanni na nuni da cewa rikicin jam'iyyar NNPP a jihar Kano ya yi ƙamari yayin da Abba Kabir Yusuf ya dauki wani mataki
- An ruwaito cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya daina daga wayar jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso
- Ana raɗe dadin cewa gwamnan ya amsa kiran masu cewa 'Abba tsaya da kafarka' wajen bijirewa magudun Kwankwasiyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Rahotanni na nuni da cewa rikincin NNPP a jihar Kano ya yi ƙamari har ya shafi alaƙar jagororin jam'iyyar.
Ana raɗe raɗin cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya daina daga wayar Sanata Rabi'u Kwankwaso kan rikicin siyasa.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa daga cikin abubuwan da suka tayar da rikicin akwai batun nada kwamishinoni.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abba ya daina daga wayar Kwankwaso
Bayan samun rikicin cikin gida, an ruwaito cewa Abba Kabir Yusuf ya daina daga wayar Rabi'u Musa Kwankwaso.
Karin bayanai na nuni da cewa Abba Kabir ya kaucewa haduwa da Rabi'u Kwankwaso domin su zauna.
Maganar nada kwamishinoni a Kano
Wani daga cikin 'ya'yan jam'iyyar ya bayyana cewa daga cikin abubuwan da suka hada Abba da Kwankwaso akwai batun kwamishinoni.
An ruwaito cewa Rabi'u Kwankwaso ne ya kawo mafi yawa daga cikin kwamishinonin jihar Kano kuma wasu sun gaza tabuka komai.
Wata majiya ta bayyana cewa Abba Kabir ya dade yana son sauke wasu kwamishinonin amma yana jin nauyin Kwankwaso.
Abba zai tsaya da ƙafarsa?
Wani kusa a NNPP ya bayyana cewa a yanzu haka Abba ya dauko hanyar tsayawa da kafafunsa a jihar Kano.
A cewar ƙusan, Abba Kabir Yusuf zai dauki matakin ne domin ya gaji da yadda madugun Kwankwasiyya ke juya shi.
Yan majalisa sun fita daga Kwankwasiyya
A wani rahoton, kun ji cewa tafiyar Kwankwasiyya ƙarƙashin jagorancin Rabiu Musa Kwankwaso ta samu koma baya a jihar Kano.
An ruwaito cewa wasu ƴan majalisar wakilai guda biyu na jam'iyyar NNPP sun sanar da ficewarsu daga tafiyar Kwankwasiyya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng