Abia: Jam'iyya Mai Mulki Ta Barar, Bakin Jam'iyyu Sun Lashe Zaben Kananan Hukumomi
- Rahotanni sun tabbatar da cewa an gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar Abia cikin lumana ba tare da tashin hankali ba
- Hukumar zaben jihar, ABSIEC ta sanar da sakamakon zaben da aka gudanar a jiya Asabar 2 ga watan Nuwambar 2024
- Hukumar ABSIEC ta tabbatar da jam'iyyar ZLP ce ta lashe zaben kananan hukumomi 15 daga cikin 17 sai kuma YPP ta cinye biyu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Abia - Hukumar zaben jihar Abia (ABSIEC) ta sanar da zaɓen kananan hukumomi da aka gudanar a jiya Asabar 2 ga watan Nuwambar 2024.
Hukumar ABSIEC ta tabbatar da jam'iyyar ZLP a matsayin wacce ta lashe zaben kananan hukumomi 15 daga cikin 17.
Abia: Yadda aka gudanar da zaben kananan hukumomi
Shugaban hukumar a jihar, Farfesa Chima George shi ya tabbatar da haka a jiya Asabar a birnin Umuahia, cewar rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun tabbatar da cewa an gudanar da zaben cikin lumana duk da al'umma ba su fito ba domin kada kuri'unsu.
Wasu na ganin hakan bai rasa nasaba da rashin kyakkyawan shiri da hukumar ABSIEC ta yi tun farko.
Rashin nasarar jam'iyyar LP ya biyo bayan rikicin cikin gida da ke addabarta musamman a jihar dama matakin kasa baki daya.
Yadda sakamakon zaben ya kasance bayan kammalawa
Farfesa George ya ce jam'iyyar YPP ce ta samu nasarar lashe zaben kananan hukumomi guda biyu.
Kananan hukumomin sun hada da Ugwunagbo da kuma Osisioma Ngwa bayan ZLP ta yi nasara a guda 15, Punch ta ruwaito.
"Mun cika ka'idar aiki bayan kaddamar da mu a ranar 5 ga watan Satumbar 2024."
"Kwata-kwata ba aiki ba ne mai sauki amma mun yi kokari wurin wayar da kan al'umma kan yanayin zabe."
- Farfesa Chima George
Kogi: An sanar da sakamakon zaben kananan hukumomi
Kun ji cewa bayan dakon sakamakon zaben kananan hukumomi a Kogi, hukumar zabe a jihar ta raba fada tsakanin jam'iyyu.
Shugaban hukumar zaben a jihar, KSIEC, Mamman Nda Eri shi ya bayyana sakamakon a jiya Asabar 19 ga watan Oktoban 2024.
Asali: Legit.ng