Siyasar Kano: Tsofaffin Yan NNPP Sun Fara Shirin Kifar da Gwamna Abba a 2027
- Wasu jagororin tafiyar Kwankwasiyya daga kananan hukumomin Kano sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC
- Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ne ya karbi mutanen a Abuja bayan sauya sheka
- Wasu daga cikin wadanda suka sauya shekar sun bayyana yadda za su kayar da NNPP a zaben shekarar 2027 mai zuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Yan siyasa a Kano sun cigaba da sauya sheka da kuma shiri a kan zaben shekarar 2027.
Wasu jagororin Kwankwasiyya a ƙananan hukumomin Tofa da Dawakin-Tofa sun sauya sheka zuwa APC.
Legit ta tatttaro yadda Sanata Barau Jibrin ya karbi yan siyasar a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yan Kwankwasiyya sun koma jam'iyyar APC
Jagoran wata kungiyar yakin neman zaben NNPP a kananan hukumomi 44, Alhaji Tijjani Abdullahi Dansalan ya koma APC.
Alhaji Auwalu Yusuf ne ya jagoranci magoya bayan NNPP zuwa APC a karamar hukumar Dawakin Tofa.
Haka zalika Isa Hamisu Moja ya jagoranci wasu yan jam'iyyar PDP a karamar hukumar Tofa zuwa APC a Abuja.
Maganar kifar da Abba a zaben 2027
Alhaji Tijjani Abdullahi Dansalan ya bayyana cewa za su kayar da jam'iyyar NNPP a Kano a zaben 2027. Ga abin da yake cewa:
"Za mu yi dabarun da muka yi wajen kawo NNPP mu kayar da ita a zaben 2027 saboda ta gaza tabuka komai."
- Tijjani Abdullahi Dansalan, tsohon dan NNPP
Barau Jibrin ya ce za su kayar da NNPP
Sanata Barau Jibrin ya bayyanawa wadanda suka sauya shekar cewa za su yi aiki tare wajen kawo cigaba a Najeriya
Barau Jibrin ya kara da cewa yawaitar masu sauya sheka alama ce da ke nuna 2027 za ta yi kyau ga APC a jihar Kano.
Hadimin Abba Kabir ya sauya sheka
A wani rahoton, Legit ta ruwaito muku cewa Sanata Barau Jibrin ya karbi da dama daga cikin magoya bayan NNPP mai mulki a ƙananan hukumomin Kano.
Daga cikin wadanda suka fice zuwa APC akwai tsohon hadimin gwamna Abba Kabir Yusuf a bangaren shari'a da wasu mutanensa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng