2027: Manyan Yan Siyasar Arewa Sun Fara Hada Kai, Suna Ganawa kan Tumbuke Tinubu

2027: Manyan Yan Siyasar Arewa Sun Fara Hada Kai, Suna Ganawa kan Tumbuke Tinubu

  • Da alamu Shugaba Bola Tinubu zai sake cin karo da matsala kan zaɓen 2027 a Najeriya duba da halin da al'umma ke ciki
  • Wasu manyan shugabannin siyasa a Arewacin Najeriya sun fara ganawa domin neman wanda za su goyawa baya a 2027
  • Yan siyasar ciki har da wasu gwamnoni na ganin cewa Tinubu ya gaza duk da goyon bayansa a 2023 da suka yi a zabe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Yayin da ake fara shirye-shiryen zaben shekarar 2027 tun yanzu, yan siyasa sun fara neman dan takarar shugaban kasa.

Rahotanni sun ce manyan yan siyasa a Arewacin Najeriya sun shiga rudani kan wanda zai maye gurbin Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Ana matsalar lantarki. 'yan Arewa sun dura kan Tinubu, sun ragargaje shi

Tinubu zai sake shiga matsala a 2027 daga Arewacin Najeriya
Wasu manyan yan siyasa sun fara neman wanda za su goyawa baya a zaben 2027 madadin Bola Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

2027: An fara neman wanda zai maye Tinubu

Tribune ta tabbatar da cewa durkushewar tattalin arziki da halin kunci musamman daga matasa ya fara jefa tsaro a zukatan yan kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tabbatar cewa shugabannin Arewa ba su jin dadi yadda ake tafiya yanzu a kasar ta kowane bangare.

Sun koka kan yadda abubuwa suka tabarbare musamman a Arewacin kasar duk da goyon baya da suka ba Tinubu.

Duba da abin da ya faru a zanga-zangar tsadar rayuwa, shugabannin na cikin fargabar faruwar hakan a nan gaba da ba zai yi kyau ba.

Manyan yan Arewa sun gaji da Tinubu

Duk da shekaru 2027 da saura, rahotanni sun ce yan siyasar sun fara neman wanda za su goyawa baya domin kalubantar Tinubu.

"Wasu manyan yan siyasa a Arewa maso Yamma na duba yiwuwar nemo wanda zai ba Tinubu ciwon kai a zaɓen 2027."

Kara karanta wannan

Nadin Minista ya jefa Tinubu a matsala, APC ta zarge shi da cin amanar jam'iyya

- Cewar wata majiya

Hadiman gwamnoni da dama a yankin sun tabbatar da haka inda suke fargaba kan zaben 2027 bayan goyon bayan Tinubu a 2023.

Wata majiya ta ce ana shirin dauko jajirtacce daga Kudu a hada da Rabiu Kwankwaso ko Aminu Waziri Tambuwal a matsayin matakinsa.

2027: Wasu na neman sake dawo da Jonathan

Kun ji cewa wasu jiga-jigan yan siyasa a Arewacin Najeriya na duba yiwuwar dawo da Goodluck Jonathan domin tsayawa takara.

Hakan bai rasa nasaba da yanayin yadda mulkin Bola Tinubu ke tafiya a halin yanzu musamman duba da halin kunci da ake ciki a fadin kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.