Jonathan Ya Fadi Wanda ya Tsaya Tare da Shi bayan Shan Kaye a Hannun Buhari a 2015

Jonathan Ya Fadi Wanda ya Tsaya Tare da Shi bayan Shan Kaye a Hannun Buhari a 2015

  • Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya tuno lokacin da ya fadi zaben da aka gudanar a 2015 a hannun Muhammadu Buhari
  • Jonathan ya bayyana irin mummunan yanayi da ya shiga kan faduwa zaben, ya ce ba abu ba ne mai sauki a rayuwa a rasa mulki
  • Tsohon shugaban kasar ya ce ba zai taba mantawa da marigayi Raymond Dokpesi ba kan yadda ya tsaya tare da shi a wancan lokaci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya yi magana kan faduwarsa zaben 2015.

Jonathan ya ce ya shiga mummunan hali bayan shan kaye a hannun tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Ana matsalar lantarki. 'yan Arewa sun dura kan Tinubu, sun ragargaje shi

Jonathan ya fadi mummunan yanayi da ya shiga bayan faduwa zaɓe a hannun Buhari
Goodluck Jonathan ya tuno faduwa zaɓe a hannun Muhammadu Buhari a 2015. Hoto: Goodluck Jonathan, Muhammadu Buhari.
Asali: Facebook

Goodluck Jonathan ya tuno zaben 2015 da Buhari

Jonathan ya bayyana haka ne yayin bikin tunawa da marigayi Raymond Dokpesi, cewar rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon shugaban kasar ya ce ba zai taba mantawa da tsohon shugaban kamfanin Daar, Raymond Dokpesi ba a rayuwarsa.

Ya ce ya shiga wani irin yanayi bayan faduwa zaben inda ya ce lamarin ba zai kwatantu ba ko kadan, Tribune ta ruwaito dazu.

Har ila yau, Jonathan ya ce marigayi Dokpesi ya kasance tare da shi inda ya ba shi shawarwari masu kyau.

Jonathan ya fadi wanda ya tsaya masa

"Ko kadan babu sauki ka rasa mulki kana kan shugabancin kasa, za ka yi tunanin duk duniya na gaba da kai ne."
"Ba zan manta ba, Dokpesi ya kira ni bayan faduwa zabe, ya ba ni shawarwari masu kyau da inganci."

Kara karanta wannan

'Idan da ina son wa'adi na 3, da na yi': Tsohon shugaban kasa, Obasanjo ya bugi kirji

"Sannan akwai wasu dattawan kasa da suka nuna damuwa kan halin da na shiga har zuwa lokacin da na fita daga damuwa."

- Goodluck Jonathan

Ana neman dawo da Jonathan sake takara

Kun ji cewa wasu rahotanni sun tabbatar da cewa akwai manya a Arewacin Najeriya da ke neman dawowar tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.

Wasu gungun yan siyasa masu ƙarfin fada a ji suna kokarin neman yardar Jonathan domin tsayawa takara a zaben 2027.

Hakan bai rasa nasaba da neman kawo cikas ga Bola Tinubu da yake wa'adinsa na farko kan shugabancin Najeriya bayan darewa mulki a 2023.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.