‘Za Ayi Aikin Banza’: Lauya Ya Kawo Shawara da Kotu Ta Hana Zaben Jihar Kano
- Kotu ta hana KANSIEC shirya zaben kananan hukumomin Kano da za a gudanar a yau 26 ga Oktoba 2024
- Alkalin kotun tarayya ya yanke hukuncin saboda rashin cancantar shugaban hukumar da wasu jami’anta
- Barista Ibrahim Arif Garba wanda masanin shari’a ne ya ba da shawarar a yi wa kotun tarayyar biyayya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kano - Ibrahim Arif Garba lauya ne kuma wanda ya saba yin magana a kan al’amuran shari'a, ya waiwayi zancen zaben Kano.
A lokacin da ‘yan kwanaki suka rage a shirya zaben kananan hukumomi a jihar Kano, sai aka ji kotun tarayya ta kawowa shirin tarnkaki.
Barista Ibrahim Arif Garba a shafinsa na Facebook, ya yi tsokaci a game da hukuncin da alkalin kotun tarayya ya yanke cikin makon jiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotu ta rusa shugabannin hukumar zabe ta jihar Kano da hujjar ‘ya ‘yan jam’iyyar NNPP ne, ta kuma hana a ba KANSIEC kayan zaben.
Menene ya kamata gwamnan Kano ya yi?
Lauyan ya ce idan da zai ari takalman Mai girma Abba Kabir Yusuf, zai nada sababbin shugabannin KANSIEC da za su shirya zabukan.
Da yake magana tun ranar Talata da dare, ya ce kyau gwamna ya sanar da sababbin shugabanni, sai ya aikawa majalisa sunayensu.
Sannan da zarar ‘yan majalisa sun karbi sunayen shugabannin na KANSIEC, Ibrahim ya ce sai a tantance su ba tare da bata lokaci ba.
“Idan ni ne Gwamna, yau zan sallami Shugabancin KANSIEC, gobe zan tura sunan sababbi Majalisa,
a gobe Majalisa za ta gama tantance su, ranar Asabar su tashi da zabe.
- Barista Ibrahim Arif Garba
Jihar Kano za ta iya shiga matsala
Tsoron da lauyan yake yi shi ne idan dai aka shiga zabe da Farfesa Sani Malumfashi, alkalai za su iya rusa duk matakin da aka dauka.
Da zarar kotu ta haramta zaben na jihar, watakila a gamu da matsala wajen aikowa kananan hukumomin kudinsu daga asusun tarayya.
Amma bayan ya yi wannan magana ne sai aka ji alkalin babban kotu a jihar Kano ya ba hukuma damar shirya zaben kananan hukumomin.
"Amma in dai aka yi zabe a haka bayan wannan hukuncin na Kotu, to zance mafi gaskia an yi wahalar banza."
Gwamnan Kano ya taka hukuncin kotu
Bayan hukuncin kotun, an rahoto Mai girma Abba Kabir Yusuf ya na cewa doka ce ta amince KANSIEC ta gudanar da zabe a jihar Kano.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi fatali da hukuncin kotun tarayyar, ya ce ba za su bar kowa ya kawo cikas a zaben ciyamomin jihar ba.
Asali: Legit.ng