A Karshe, Bola Tinubu Ya Maye Gurbin Betta Edu, Ya Nada Sabon Ministan Jin Ƙai

A Karshe, Bola Tinubu Ya Maye Gurbin Betta Edu, Ya Nada Sabon Ministan Jin Ƙai

  • A karshe Bola Ahmed Tinubu ya maye gurbin Betta Edu, tsohuwar ministar harkokin jin kai da yaƙi da talauci
  • Shugaban ƙasar ya amince da naɗin Dr Nentawe Yilwatda, ɗan asalin jihar Filato a matsayin sabon minista na jin ƙai
  • Tinubu ya dakatar da Edu ne tun a watan Janairu bisa zargin karkatar da wasu kuɗi zuwa asusun da bai dace ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

State House, Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya maye gurbin Betta Edu, dakatacciyar ministar harkokin jin ƙai da yaye talauci.

Shugaban ƙasar ya naɗa Dr Nentawe Yilwatda a matsayin sabon ministan jin ƙai, wanda zai maye gurbin Betta Edo bayan dogon lokaci da dakatar da ita.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya ɗauko Ministan Buhari, ya naɗa shi a muƙami bayan korar ministoci

Dr Nentawe Yilwatda da Betta Edu
Bola Ahmed Tinubu ya nada Dr Nentawe Yilwatda a matsayin wanda zai maye gurbin Betta Edu Hoto: @Henryhoomen1
Asali: Twitter

Hakan dai na kunshe ne a sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta wallafa a shafin X yau Laraba, 23 ga watan Oktoba, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Betta Edu ta rasa muƙaminta

A watan Janairu, 2024 Tinubu ya dakatar da Betta Edu tare da ba da umarnin a binciki yadda aka tura Naira miliyan 585.2 zuwa asusun banki na wani ma’aikaci.

Tinubu ya kuma umarci hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta gudanar da bincike mai zurfi kan dukkan hada-hadar kudi a ma'aikatar karkashin Edu.

Betta Edu ta musanta zargin da ake mata

Tun da farko dai Betta Edu ta musanta zargin da ake mata na karkatar da wasu kuɗaɗe zuwa asusun kai-da-kai.

A lokacin ofishin ministar ya fito ya bayyana cewa Edu ya amince da tura kuɗin zuwa asusun mutumin ne domin rabawa ƴan Najeriya masu ƙaramin karfi.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya aika muhimmin saƙo ga ministoci 5 da ya kora daga aiki

Tinubu ya maye gurbin Edu a ma'aikatar jin ƙai

A halin yanzu, Bola Tinubu ya maye gurbin Edu, ya naɗa Dr Nentawe Yilwatda a matsayin sabon ministan harkokin jin ƙai.

Wannan naɗi na cikin garambawul din da shugaban ƙasa ya yi a majalisar zartaswa ta ƙasa, inda ya kori wasu ministoci kuma ya naɗa sababbi.

Tinubu ya ba tsohon ministan Buhari muƙami

A wani rahoton kuma Bola Tinubu ya amince da naɗin Sunday Dare a matsayin mai ba da shawara kan harkokin sadarwa da wayar da kan jama'a.

Dare dai ya yi aiki a matsayin ministan matasa da bunkasa harkokin wasanni a gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262