"Ko da Jami'an Tsaro ko babu, za a Yi Zabe:" Majalisar Dokokin Kano ga Kotu

"Ko da Jami'an Tsaro ko babu, za a Yi Zabe:" Majalisar Dokokin Kano ga Kotu

  • Majalisar dokokin Kano ta yi watsi da hukuncin babbar kotun tarayya kan dakatar da zaben kananan hukumomi a jihar
  • Shugaban masu rinjaye na majalisa, Lawan Hussaini Dala a martaninsa ya ce hukuncin kotun bai ba su mamaki ba
  • Ya jaddada cewa ko da taimakon jami'an tsaro ko babu, za a gudanar da zaben kananan hukumomi a fadin jihar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Majalisar dokokin Kano ta yi martani ga hukuncin babbar kotun tarayya na korar shugaban hukumar zabe na jihar (KANSIEC), Farfesa Sani Malumfashi daga mukaminsa.

Kotu ta kuma umarci hukumar zabe ta kasa (INEC) da kar ta ba KANSIEC kayan gudanar da zaben kananan hukumomi da za a yi a ranar Asabar 26 Oktoba, 2024.

Kara karanta wannan

Zaben kananan hukumomi zai lakume kudi, gwamna zai kashe Naira biliyan 2

Majalisa
Majalisa ta ce zaben kananan hukumomin Kano ba fashi Hoto: Hon Jibril Ismail Falgore
Asali: Facebook

A wani bidiyo da Kwankwason Tuwita ya wallafa a shafinsa na X, shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin Kano, Lawan Hussaini Dala ya yi fatali da hukuncin kotun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Zaben Kano babu fashi:" Majalisar dokoki

Majalisar dokokin Kano ta bayyana cewa hukuncin da babbar kotun tarayya ta zartar da cewa ya ci karo da hukuncin kotun kolin kasar nan.

Ya ce hukuncin kotun kolin kasar nan ya nuna bukatar kowace jiha ta gudanar da zabe kafin karshen watan da mu ke ciki,

Majalisa ta nemi taimakon jami'an sa kai

Shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin Kano, Lawan Hussaini Dala ya ce ko babu gudunmawar jami'an tsaro za a gudanar da zaben kananan hukumomi.

Ya nemi taimakon yan jam'iyyar NNPP da jami'an sa kai da su fito tare da bayar da kariya a zaben da za a gudanar ranar Asabar mai zuwa.

Kara karanta wannan

An zo wurin: Kotu ta yi zama kan zargin Ganduje da almundahana, ta shirya yanke hukunci

Kano: Kotu ta kori shugaban hukumar zabe

A wani labarin kun ji cewa babbar kotun tarayya karkashin jagorancin Mai Shari'a Simon Ameboda ta dakatar da shugaban hukumar zabe mai zaman kanta a Kano, Farfesa Sani Malumfashi.

A karar da APC ta shigar gabanta, kotun ta ce an yanke hukuncin ne bisa da tabbatar da karya dokokin nada shugaban hukumar da wasu kusoshi a KANSIEC kasancewarsu yan jam'iyyar NNPP.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.