‘Yan APC da Suka Koma Kuka da Gwamnati saboda Tsadar Rayuwa a Zamanin Tinubu
Abuja - Akwai wasu daga cikin ‘ya ‘yan jam’iyyar APC mai mulki da a bari ba wajen kokawa da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kwanaki kadan bayan Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya gaji Muhammadu Buhari, aka samu karin matsananciyar rayuwa.
Rahoton nan ya tattaro jerin manyan ‘yan APC da aka ji sun soki gwamnatinsu ko dai su na neman a gyara yadda ake tafiya.
'Yan APC da suka caccaki mulkin Tinubu
1. Muhammad Ali Ndume
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A lokuta dabam-dabam an ji Muhammad Ali Ndume mai wakiltar Borno ta kudu a majalisar dattawa ya na sukar gwamnatin APC.
Daily Trust ta rahoto yadda yawan taba shugaba Bola Tinubu da sanatan yake yi ya jefa sa cikin matsala a jam’iyyar APC da majalisa.
2. Rotimi Amaechi
Duk da ya na cikin manya a APC kuma har ya nemi tikitin tsayawa takarar shugaban kasa, an ji Rotimi Amaechi yana kukan tsadar rayuwa.
Sai dai za a iya cewa tsohon ministan sufurin ya yi watsi da al’amuran APC tun kafin 2023, ta kai ana zarginsa da taimakawa APC a zaben bara.
3. Babachir David Lawal
Injiniya Babachir David Lawal ya rike sakataren gwamnatin tarayya kuma ya na cikin wadanda ake ji a baya su na yabon Bola Tinubu.
Tun da Tinubu ya zabi musulmi ya zama abokin tafiyarsa, Babachir yake sukarsa kuma har yau ya kan yi kaca-kaca da gwamnatin APC.
4. Salihu Muhammad Lukman
Salihu Muhammad Lukman ya taba zama shugaban APC a shiyyar Arewacin Najeriya, wannan bai hana shi taba gwamnatinsu ba.
Ko da yake a yanzu ya yi watsi da jam’iyya mai mulki, amma ko a lokacin da yake nan, Punch ta rahoto shi ya na tir da mulkin Tinubu.
5. Otu Ita Toyo
Kwanaki labarai suka rika yawo cewa wani jagora a APC a Akwa Ibom, Otu Ita Toyo ya fito yana Allah-wadai da Mai girma Bola Tinubu.
A lokacin da ake ta surutu kan badakalar satifiket, sai aka ji Otu Ita Toyo ya na cewa shugaban kasar ya bata martabar Najeriya a duniya.
6. Joe Igbokwe
Kafin yanzu Joe Igbokwe ya na cikin manyan masu kare Bola Tinubu, an san shi wajen rashin saurarawa masu taba APC a jihar Legas.
Ba a dade da fara mulki ba sai ga shi Igbokwe ya na wayyo Allah, ya na mai kira ga shugaban kasa ya canza tsare-tsaren da ya kawo.
An ga Bola Tinubu a Ingila
Kwanaki kusan 10 da tafiya kasar Ingila, rahoto ya bayyana cewa an ga hotunan shugaba Bola Ahmad Tinubu ya na hutawa a gidansa.
Ibrahim Kabir Masari wanda yana cikin na hannun daman shugaban ya iya ganawa da shi, ya ce daga nan Tinubu zai ziyarci kasar Faransa.
Asali: Legit.ng