Yadda ‘Yan Siyasar Jihar Kano 4 Suka Zagaya Kujera 1 cikin Shekaru 8 a Gwamnatin Tarayya
- Muhammadu Buhari ya fara jawo Kawu Sumaila ya zama mai taimaka masa kan harkokin ‘yan majalisar wakilai
- Tun daga wancan lokaci har zuwa yau, wannan kujera ta na ta yawo tsakanin ‘yan siyasar Kano ta tsakiya da ta Kudu
- Hon. Umar Ibrahim El-Yakub da Hon. Nasiru Illa sun rike mukamin, sai Bashir Lado kuma ya samu makamancinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Kamar an yi wa ‘yan siyasar Kano alkawarin kujerar mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin majalisar tarayya.
A cikin shekarun da ba su kai 10 ba, an samu mutane daga jihar Kano da shugaban kasa ya ba wannan babbar kujera a gwamnati.
Legit Hausa ta bibiyi yadda Muhammadu Buhari da Bola Tinubu suka rika dauko masu ba da shawara kan aikin majalisa daga Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan Kano da suka zama hadimai a harkar majalisa
1. Kawu Sumaila
Daily Trust ta tuna da Muhammadu Buhari ya nada Kawu Sumaila a matsayin mai ba shi shawara kan harkokin majalisar (wakilai) a 2015.
Kafin nan ‘dan siyasar ya wakilci Takai da Sumaila a majalisar tarayya. Shekaru bayan barin kujerar ya zama Sanatan kudancin Kano.
2. Umar Ibrahim El-Yakub
Lokacin da Sumaila ya sauka daga kujerarsa, ya tafi neman takara a 2019, Premium Times ta ce an canza shi da Hon. Umar Ibrahim El-Yakub.
Umar Ibrahim El-Yakub ya na rike da kujerar mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara sai aka zabe shi cikin Ministoci a 2022.
3. Nasiru Illa
Har ila yau, daga jihar Kano dai aka maye gurbin Umar Ibrahim El-Yakub wanda Garba Shehu ya ce ya zama Ministan harkokin gidaje.
Sanarwar da aka fitar ta ce Nasiru Illa ya wakilci Tarauni a majalisar tarayya kuma kwararren akanta ne da ya yi karatu har a Ingila.
4. Basheer Lado
Shi kuma Bola Tinubu da ya zama shugaban kasa, ya zabi Basheer Lado ya zama mai ba shi shawara a kan sha’anin majalisa (ta dattawa).
Sanata Basheer Lado ya wakilci Kano ta tsakiya a PDP daga 2011 zuwa 2015. Rabiu Kwankwaso ya doke shi, daga baya sai ya dawo APC.
NNPP a rikicin siyasar Kano
Duk yadda Abba Kabir Yusuf yake da Rabiu Musa Kwankwaso, rahoto ya zo cewa ana so a shiga tsakaninsu a siyasa a 'yan kwanakin nan.
‘Yan kungiyar Abba tsaya da kafanka sun ce dole sai gwamnan Kano ya rabu da Madugun Kwankwasiyya idan ya na so ya yi aiki a ofis.
Asali: Legit.ng