Wata sabuwa: Jam'iyyar APC ta yaudare ni - Tsohon Sanatan Kano ta tsakiya Hon Bashir Garba Lado

Wata sabuwa: Jam'iyyar APC ta yaudare ni - Tsohon Sanatan Kano ta tsakiya Hon Bashir Garba Lado

- Tsohon Sanatan Kano ta tsakiya Bashir Garba Lado ya bayyana cewa jam'iyyar APC ta na so ta yaudare shi ne

- Ya bayyana cewa yana zaman shi a jam'iyyar PDP suka zo suka rarrashe shi ya bar PDP, bayan sun yi masa alkawarin bashi kujerar minista

- Ya ce abin takaici shine ganin yadda Buhari ya fitar da sunayen ministoci babu shi a ciki

Tsohon Sanatan Kano ta tsakiya Hon Bashir Garba Lado Alheri ya bayyanawa manema labarai cewa babbar jam'iya mai mulki ta APC tana son ta yaudareshi bayan tayi amfani dashi ta samu nasara.

Bashir Lado dai dan babbar jam'iyar adawa ne ta PDP, kafin daga baya jam'iyar APC tayi masa alkawarin bashi tikitin tsayawa takarar Sanatan Kano ta tsakiya mutukar ya dawo jam'iyar APC.

Bayan ya dawo jam'iyar ne kuma, jam'iyar ta kara shiga zawarcin Sardaunan Kano Malam Ibrahim Shekarau, inda shima tayi masa alkawari irin wanda ta yiwa Lado na tikitin takarar Sanatan Kano ta tsakiya.

Lokacin da jam'iyyar ta nemi Lado, ya nuna rashin amincewarsa ga hakan inda ya nemi da a gudanar da zaben fitar da gwani kato bayan kato kamar yadda jam'iyar ta umarta.

KU KARANTA: Tirkashi: Rashin sunan Ali Nuhu a cikin jerin Ministocin da Buhari ya fitar ya jawo kace - nace

Lokacin wasu jiga-jigan jam'iyyar APC ciki harda shugaban jam'iyar na kasa Comrade Adams Oshiomole da gwamna Ganduje sun rarrashe shi cewa yayi hakuri ya janyewa Shekarau, inda shi kuma suka yi masa alkawarin cewa za su tura sunansa wajen Buhari ya ba shi kujerar Minista mutukar jam'iyar ta APC ta samu nasarar lashe zaben shugaban kasa , sannan a lokacin ne suka nada shi shugaban yakin neman zaben Buhari na jihar kano.

"Nayi iya kokarina da dukiya ta da karfina da magoya bayana har takai jam'iyarmu ta APC ta samu nasara, amma a karshe sai gashi cikin sunayen ministocin da Buhari ya aikewa majalisa babu sunana a ciki," in ji Lado.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng