Gwamnan a Arewa Ya Sanya Dokar Takaita Zirga Zirga Ta Awanni 12, Bayanai Sun Fito

Gwamnan a Arewa Ya Sanya Dokar Takaita Zirga Zirga Ta Awanni 12, Bayanai Sun Fito

  • GwamnatinKaduna na ci gaba da shirye-shiryen gudanar da zaben ciyamomi da na kansilolin kananan hukumomi 23 na jihar
  • Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida ta Kaduna, Samuel Aruwan ya ce an sanya dokar takaita zirga zirgar mutane a fadin jihar
  • Domin gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali, Aruwan ya ce dokar za ta fara aiki ne daga karfe 6 zuwa karfe 7 na yammacin Asabar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Majalisar tsaro ta jihar Kaduna ta sanya dokar hana zirga-zirga a fadin jihar daga karfe shida na safe zuwa karfe bakwai na yamma a ranar Asabar, 19 ga Oktobar 2024.

Dokar hana zirga-zirgar na zuwa ne kasa da sa'o'i 24 a gudanar da zaben ciyamomi 23 da na kansiloli 255 da aka shirya gudanarwa a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Anambra: INEC ta sanya lokacin gudanar da zaben gwamna, ta fadi shirin da ta yi

Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar takaita zirga zirga a gobe Asabar
Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar hana zirga zirga a ranar zaben ciyamomi. Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

An sanya dokar takaita zirga zirga

Bayanin hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da babban mai tallafawa gwamnan Kaduna ta fuskar yada labarai, Abdallah Yunus Abdallah ya fitar a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar na dauke da sa hannun kwamishinan ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida ta jihar Kaduna, Samuel Aruwan.

Sanarwar ta ce an sanya dokar takaita ziyarga zirga a fadin jihar ne domin wanzar da zaman lafiya yayin gudanar da zaben da kuma bayansa.

Samuel Aruwan ya ce an hana zirga-zirgar ababen hawa da kuma harkokin kasuwanci a cikin wa'adin dokar (6 na safe zuwa 7 na yammacin ranar Asabar).

Gwamnati ta nemi hadin kan jama'a

Sanarwar ta ce:

"Mutanen da ke aiwatar da muhimman ayyuka ne kaɗai aka ware daga wannan dokar, kuma za su iya yin zirga zirga ne ta hanyar amfani da shaidar tantancewa."

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya bayyana babbar matsalar Najeriya da Tinubu ya fara magancewa

Don haka gwamnatin Kaduna ta shawarci ‘yan jihar da su guji ayyukan da za su kawo cikas ga zaman lafiyar al’umma ko kuma gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali.

An kuma yi kira ga jama’a da su gaggauta kai rahoton duk wani abu da aka gani da ke barazana ga doka da oda ga hukumomin tsaro, ba tare da daukar doka a hannunsu ba.

Kaduna: Wa'adin ciyamomi zai kare 2024

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumr zaben Kaduna (KAD-SIECOM) ta sanya Asabar, 19 ga Oktoba matsayin ranar da za a gudanar da zaben ciyamomin jihar.

KAD-SIECOM ta lura cewa ciyamomi da kansilolin da ke mulki yanzu sun shiga ofis ranar 1 ga Nuwamba, 2021 kuma wa'adinsu na shekara uku zai kare ranar 31 ga watan Oktoba, 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.