Albashi da Alawus: Sanatan APC Ya Bayyana Miliyoyin da Ake Tura Masa a duk Wata
- Sanata mai wakiltar Abia ta Arewa, Orji Kalu, ya ce yana karbar Naira miliyan 14 duk wata a matsayinsa na dan majalisar dattawa
- Tsohon gwamnan jihar Abia ya ce Naira miliyan 14 da yake samu duk wata ba ya isarsa biyan bukatun mazabarsa da na ma’aikatansa
- A zantawarmu da wasu 'yan Arewa, sun bukaci 'yan majalisu da su ji tsoron Allah kan yadda suke kashe kudaden al'ummar mazabunsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Sanata Orji Uzor Kalu, mai wakiltar Abia ta Arewa, ya bayyana cewa ya na karbar Naira miliyan 14 duk wata a matsayinsa na dan majalisar tarayya.
Sanata Kalu ya kuma yi watsi da ra’ayin cewa ‘yan majalisar dokokin Najeriya na rayuwa cikin walwala yayin da talakawa ke shan wahala.
Albashin Sanata Orji Kalu a kowane wata
Ya bayyana hakan ne a zantawarsa da Channels TV, inda ya fayyace cewa wannan kudin ya shafi dukkanin kudaden da yake kashewa da ya hada da albashin ma’aikatansa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yayin tattaunawar, sanatan ya ce:
“Ina samun Naira miliyan 14 a duk wata. Wannan kudin ya shafi komai na rayuwata da na mazabata da kuma na albashin masu yi mani hidima.
Albashin N14m bai isan Sanata Kalu
Sanata Kalu, wanda tsohon gwamnan jihar Abia ne, ya jaddada cewa da kyar Naira miliyan 14 ke wadatar da ayyukan da ya rataya a wuyansa.
Daga cikin ayyukan gaban 'dan majalisar akwai tafiya mazabarsa da kula da ofishinsa.
Ce-ce-ku-ce kan albashin sanatoci
Wannan bayani ya ba da haske game da gaskiyar kudin da sanatoci ke samu a duk wata, wanda galibi ake boyewa kuma ake ci gaba da ce ce ku ce a kai.
Sanatan ya ce yin wannan jawabin da yake samu na da nufin inganta gaskiya da kuma kalubalantar ra'ayin jama'a game da albashin 'yan majalisa ke samu.
An nemi 'yan majalisu su ji tsoron Allah
A zantawarmu da wasu 'yan Arewa, sun nuna mamaki yadda Sanata Kalu ya ke ikirarin cewa albashin N14m ya yi masa kadan, ba tare da la'akari da halin da talaka ke ciki ba.
Wani dan kasuwa, Al'Amin Ibrahim ya ce babu gaskiya kan albashin sanatoci tunda a baya wani ya fito ya ce N21m ne ake ba shi duk wata.
Al'Amin ya ce ko ma dai N14m ne din ake biyan sanatoci, akwai bukatar su ji tsoron Allah saboda kaso mai tsoka na kudin ba hakkinsu ba ne, na 'yan mazabarsu ne.
Wani magidanci, Malam Iliyasu Karami ya ce abin takaici ne yadda wasu 'yan majalisu ke daina ziyartar al'ummarsu daga lokacin da suka dare kujerar mulki.
Malam Iliyasu ya ce akwai mazabun da ko Naira miliyan daya ba sa amfani da ita daga albashin sanatocin, haka kuma babu wani aikin mazabar da suke yi da kudin.
"Ina karbar N21m" - Sanata Sumaila
A wani labarin, mun ruwaito cewa Abdurrahman Kawu Sumaila na jam’iyyar NNPP ya bayyana cewa yana karbar albashi da alawus alawus har Naira miliyan 21 duk wata.
Sanata Kawu Sumaila mai wakiltar Kano ta Kudu a majalisar dattawa ta 10, ya ce ‘yan majalisar tarayya ba sa sanya wa kansu albashi da alawus da ya wuce kima.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng