Anambra: INEC Ta Sanya Lokacin Gudanar da Zaben Gwamna, Ta Fadi Shirin da Ta Yi

Anambra: INEC Ta Sanya Lokacin Gudanar da Zaben Gwamna, Ta Fadi Shirin da Ta Yi

  • Hukumar INEC ta bayyana cewa za a gudanar da zaben gwamnan jihar Anambra a ranar Asabar 8 ga watan Nuwamba, 2025
  • Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Abuja a taron tuntubar juna da jam’iyyun siyasa
  • Ya ce jam'iyyun siyasa za su gudanar da zaben fitar da gwani daga 20 ga Maris 2025 zuwa 10 ga Afrilu 2025 tare da yin bayani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Yayin da take shirin zaben Ondo, hukumar NEC ta bayyana lokacin da za a gudanar da zaben gwamna a jihar Anambra.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar ta ce za ta gudanar da zaben gwamnan Anambra a ranar 8 ga watan Nuwambar 2025.

Kara karanta wannan

APC ta tsorata, ta janye daga fafatawa a zaben kananan hukumomi, ta fadi dalili

INEC ta yi magana kan ranar da za a gudanar da zaben gwamnan jihar Anambra
INEC ta sanya ranar da za ta gudanar da zaben gwamnan Anambra. Hoto: @inecnigeria
Asali: Twitter

INEC ta sanya ranar zaben Anambra

Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a ranar Alhamis a Abuja kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farfesa Yakubu ya yi magana ne a wani taro na musamman da ya yi da shugabannin jam'iyyun siyasar kasar masu rajista, wanda ya ce zai kasance na karshe a 2024.

Shugaban hukumar ya ce za a buga sanarwar zaben a hukamance a ranar 13 ga Nuwamba 2024.

Hukumar INEC ta fadi shirin da ta yi

Jaridar TheCable ta rahoto Farfesa Yakubu ya ce INEC na sa ran jam'iyyu za su gudanar da zabukan fitar da gwani na daga ranar 20 ga Maris 2025 zuwa 10 ga Afrilu, 2025.

Ya ce za a bude shafin dora bayanan ɗan takara da ƙarfe 9.00 na safe a ranar 18 ga Afrilu 2025 kuma za a rufe da ƙarfe 6.00 na yammacin ranar 12 ga Mayu 2025.

Kara karanta wannan

Rikicin jam'iyya: An bayyana lokacin da Damagum zai sauka daga shugaban PDP

INEC ta ce za a fitar da sunayen 'yan takara na karshe a ranar 9 ga Yunin 2025, yayin da za a fara yakin neman zabe daga ranar 11 ga Yuni.

Za a yi ta kamfen zama gwamna har zuwa daren ranar Alhamis 6 ga Nuwamba 2025.

Soludu ya lashe zaben Anambra

A wani labarin, mun ruwaito yadda Farfesa Charles Soludu na jam'iyyar APGA ya lashe zaben gwamnan jihar Anambra da aka yi 2021.

Soludo, tsohon gwamnan babban bankin Nigeria CBN ya samu jimillar kuri'u 112,229, ya doke 'yan takarar da ke biye masa daga PDP da APC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.