Gwamnoni 4 da Ake Zargi da Rushe Kadarori a Jihohinsu kan bambancin siyasa
A siyasar Najeriya ana yawan samun matsala tsakanin tsohon gwamna da ya bar mulki da kuma wanda ya dare kan kujera saboda wasu dalilai.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Mafi yawan sababbin gwamnonin suna ɓullo da wasu abubuwa musamman na daukar fansa kan wadanda suka bar kujerun ko dan saboda adawa ko wata matsala tsakaninsu.
Gwamnoni da ake zargi da rushe-rushe
Akwai wasu gwamnoni da ake zargin sun yi rusau musamman saboda su kuntatawa abokan gaba a jihohinsu, cewar rahoton Thisday.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit Hausa ta duba wasu gwamnoni da ake zargin sun yi rusau saboda adawar siyasa.
1. Gwamna Abba Kabir - Kano
Hawansa karagar mulki ke da wuya Abba Kabir ya bullo da maganar rusau kan wasu kadarori da yake zargin an gina ba bisa ka'ida ba.
Abba ya bukaci rushe duka wuraren da aka gina ba bisa ka'ida ba musamman wadanda tsohuwar gwamnatin Abdullahi Ganduje ta siyar.
Rusau da Abba Kabir ya yi ya jawo ce-ce-ku-ce da ake ganin kawai saboda bambancin siyasa ne da kuma jawo asarar dukiyoyin al'umma.
2. AbdulRahman AbdulRazak - Kwara
A makon da ya gabata, gwamnatin jihar Kwara ta rushe wani babban kanti mai suna 'Crystal Palace' da ke Ilorin.
Tsohon gwamnan Kwara, Bukola Saraki ya zargi gwamnatin jihar da rushe shagon saboda adawar siyasa da ke tsakaninsa da Gwamna AbdulRahman AbdulRazak, cewar The Nation.
Wanda aka rushewa shagon, Moshood Mustapha tsohon hadimi ne kuma kwamishina a mulkin Bukola Saraki.
3. Godwin Obaseki - Edo
Jim kadan bayan dawowa karagar mulkin jihar Edo a 2020, Gwamna Obaseki ya fara takun-saka da tsohon mataimakin gwamnan jihar, Pius Odubu da jiga-jigan APC da suka ki goyon bayansa.
Obaseki ya kwace takardun filayen da tsohon gwamna, Adams Oshiomhole ya ba su kafin barin gidan gwamnati a matsayin kyautar rabuwa.
Punch ta ruwaito cewa Gwamnan ya kwace takardun mallakar filayen ciki har da wanda shi ma aka ba shi.
4. Hope Uzodinma - Imo
Ba tare da bata lokaci ba bayan shiga ofis, Gwamnan Imo, Hope Uzodinma ya rushe kadarar hadimin tsohon gwamnan jihar, Rochas Okorocha, cewar PM News.
Hadimin Okorocha mai suna Sam Onwuemeodo ya zargi daukan matakin saboda bambancin siyasa da ke tsakaninsa da Uzodinma.
Gwamna Abba Kabir ya fice daga Kano
Kun ji cewa Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya shilla zuwa birnin Tarayya Abuja a ranar Talata, 15 ga watan Oktoban 2024.
Abba Kabir Yusuf ya fice daga jihar ne yayin da ake ci gaba da rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar NNPP mai mulki a Kano.
Ficewar gwamnan dai na zuwa ne a daidai lokacin da jagoran NNPP na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso, yake a cikin jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng