Yar’adua, Saraki da Sauran Gidajen Siyasa 10 da Suka Fi Shahara a Najeriya

Yar’adua, Saraki da Sauran Gidajen Siyasa 10 da Suka Fi Shahara a Najeriya

Akwai wasu gidaje da su ka yi suna da siyasa, a duk lokacin da aka ambaci ‘yan gidan, abin da yake zuwa ran mutane kenan.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

A rahoton nan, mun yi kokarin tattaro wasu gidajen da suka yi fice a harkar siyasa kusan daga 1960 da aka mallaki ‘yancin kai.

siyasa
Fitattun gidajen siyasa Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Gidajen siyasa da suka yi suna

1. Yar’adua a siyasar Najeriya

Ana da labarin yadda Musa Yar’adua wanda ya yi Minista a gwamnatin Tafawa Balewa ya haifo manyan ‘yan siyasa da ake ji da su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Janar Shehu Yar’adua ya zama gwarzo a siyasa bayan ritaya daga soja kuma haka aka samu ‘ya ‘yansa da ‘yanuwansa sun bi sahu.

Kara karanta wannan

Mutane 16 ‘yan gida 1 da suka shiga fagen siyasa kuma suka shahara a Najeriya

A 2007 aka samu Ummaru daga gidan Yar’adua ya zama shugaban kasa. Bayan nan sun fito da Ministan tsaro da Sanata a Katsina.

2. Siyasar Waziri Ibrahim

Daily Trust ta kawo rahoton da ya nuna tasirin gidan Waziri Kolo Ibrahim a siyasa tun bayan da ya nemi mulkin Najeriya a GNPP a 1979.

Alhaji Waziri Kolo Ibrahim shi ne ya haifi Khadijah Bukar wanda ta yi kwamishina da Minista kuma yanzu ta koma majalisar wakilan tarayya.

Babban ‘dan siyasar ya kasance ya hada surukunta da marigayi Sanata Bukar Abba Ibrahim.

3. Gidan Saraki a Kwara

An yi shekara da shekaru gidan Saraki su na rike da siyasar jihar Kwara a karkashin jagorancin Abubakar Olusola Saraki (1933-2012).

Olusola Saraki ya yi sanadiyyar da Adamu Attah, Cornelius Adebayo, Mohammed Lawal da ‘dansa su ka zama gwamnonin Kwara.

Bayan Bukola Saraki da ya yi fice a Najeriya, kanwarsa watau Gbemisola Saraki ta rike kujeru kamar na Ministar sufuri da Sanata.

Kara karanta wannan

An samu mutumin farko da aka gani da Tinubu a Ingila, ya fadi halin da ake ciki

4. Richard Akinjide

Daga tsatson Richard Akinjide (SAN) an samu manyan ‘yan siyasa. Lauyan ya fara shahara saboda rawar da ya taka a lokacin Shehu Shagari.

Kafin nan ya na cikin ministocin Abubakar Tafawa Balewa. Bayan shekaru 40, PDP ta ba diyarsa, Oloye Jumoke Akinjide, ministar harkokin Abuja.

5. Jikokin Adelabu sun shiga siyasa

A yankin na Kudu maso yamma, akwai gidan Adegoke Adelabu wanda shi ma ya yi Minista a 1955 kuma ya jaoranci adawa kafin rasuwa a 1958.

A 2023 jikansa Adebayo Adelabu, tsohon mataimakin gwamnan CBN ya nemi kujerar gwamnan jihar Oyo. Yanzu Ministan makamashi ne a kasa.

6. Shinkafi da ‘ya ‘yansa a siyasa

Umaru Aliyu Shinkafi ya kafa sunansa a siyasar Najeriya kafin rasuwarsa. Mahmud Aliyu Shinkafi wanda kaninsa ne ya yi gadonsa a Zamfara.

‘Ya ‘yansa irinsu Fatima Umaru Shinkafi, Dr Zainab Atiku Bagudu da Hadiza Abdulaziz Yari kusan duk sun shiga harkar ko sun auri ‘yan siyasar.

Kara karanta wannan

Boko haram: Sanata Ndume ya fadi gaskiya kan kai masa hari

7. Zuri’ar Olusegun Obasanjo a siyasa

Kowa ya san cewa Cif Olusegun Obasanjo ya shafe sama da shekaru 10 a matsayin shugaban Najeriya a zamanin mulkin soja da kuma farar hula.

Diyarsa Iyabo Obasanjo Bello da ta taba sukarsa ta taba zama Sanata a Ogun. Danuwanta, Olujonwo Obasanjo ya taimakawa APC a 2019 da 2023.

8. Rabiu Musa Kwankwaso

A zaben 2023, tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya yi nasarar ganin surukinsa, Abba Kabir Yusuf ya karbi mulki a NNPP.

Akwai yaron cikinsa, Mustafa Kwankwaso ya zama Kwamishina. Haka zalika akwai ‘yanuwansa irinsu Yahaya Kwankwaso a cikin fagen.

9. Ojukwu da ‘yan gidansa

Bianca Ojukwu wanda ta auri Odumegwu Ojukwu ta jarraba farin jininta da ta nemi takarar Sanatar Anambra ta Kudu a jam’iyyar APGA.

Shi kan shi Marigayi Ojukwu ya taba yin takarar Sanata a NPN a 1979. Yanzu yaron da haifa, Emeka Ojukwu Jnr ya na tare da APC mai-ci.

Kara karanta wannan

Neman Tazarce a 2027: Manyan 'yan siyasar Kano da ke goyon bayan Shugaba Tinubu

10. ‘Ya ‘yan Shagari a harkar siyasa

Marigayi Bala Shagari zai iya shiga cikin ‘yan siyasa, ya wakilci Yabo, Shagari da Tambuwal da za a shirya kundin tsarin mulki a 1988.

Shi kuwa kaninsa, Mukhtar Shagari cikakken ‘dan siyasa ne wanda ya nemi gwamnan Sokoto, kwanaki ya bar PDP zuwa APC mai-ci.

11. Siyasar Bola Tinubu

Sunan Bola Tinubu ya zagaye duniya a yanzu a sanadiyyar siyasarsa. Hatta matar shugaban kasar ta taba zama Sanatar yammacin Legas.

‘Ya ‘yansa irinsu Folashade Tinubu-Ojo da Seyi Tinubu sun kama hanyar bin sahu. Akwai surukan Tinubu da ke da mukamai a gwamnati.

'Yan gida daya a fagen siyasa

Ku na da labari cewa Rabiu Kwankwaso ya na da kani wanda ya taba zama shugaban matasan Kwankwasiyya na Kasa a baya.

Ahmad Babba-Kaita ya yi takara da yayansa watau Kabir Babba-Kaita wajen zama Sanata a Katsina, irin haka ta faru a jihar Anambra.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng